Bayan dowarwarsa shugaba Buhari ta kada hantar 'yan wawa

Bayan dowarwarsa shugaba Buhari ta kada hantar 'yan wawa

- Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan ya kammala hutunsa a birnin Landan

- Bayan ya dawo, shuagaban kasa ya rubuta wasika domin sanar da majalisar tarayya cewa a shirye yake ya cigaba da aiki

- Shugaban kasar yace yanzu ya huta sosai komai a shirye yake ya cigaba da daure masu satar dukiyar gwamnati

A jiya Asabar shugaba Muhammadu Buhari ya jadada aniyarsa na cigaba da yaki da dukkan masu satar kudaden talakawa domin ya jefa su gidan yari.

Buhari ya furta wannan maganar ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan jirginsa ya sauka a filayen tashin jirage na Nnamdi Azikwe a Abuja kamar yadda This Day ta wallafa.

Shugaba Buhari ya fadi wata magana da ta kada hantar 'barayin gwamnati'
Shugaba Buhari ya fadi wata magana da ta kada hantar 'barayin gwamnati'

"Zan cigaba da aiki tukuru don gannin cewa duk wadanda suka sace kadaden Najeriya sun samu masauki a gidan yari," inji shugaba Buhari.

DUBA WANNAN: Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta

A lokacin da yake bayyana yadda yake ji bayan dawowarsa daga hutun a birnin Landan, shugaba Muhammadu Buhari ya shaidawa manema labarai a filin jirgin saman cewa yana jinsa garau kuma ya watsake.

Jim kadan bayan isowarsa Najeriya, shugaba Buhari ya rubuta wasika ga majalisar tarayya don sanar dasu cewa ya dawo kuma a shirye yake ya kama aiki a matsayinsa na shugaban kasar Najeriya.

A lokacin da shugaba Buhari ke hutu, mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya karbi ragamar mulkin kasar kamar yadda aka saba duk lokacin da shugaban kasar zaiyi tafiya.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku ta'aziyyar da shugaba Muhammadu Buhari ya yi game da rasuwar tsohon sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan wanda ya rasu a ranar 18 ga watan Augusta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel