Osinbajo ya saka hannu a kan wasu sabbin muhimman dokoki 3

Osinbajo ya saka hannu a kan wasu sabbin muhimman dokoki 3

Mukadashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya saka hannu kan wasu dokoki guda uku domin fara aiki dasu a matsayin dokoki.

Mai taimakin Osinbanjo na musamman a fannin yada labarai, Laulu Akande, ne ya fitar da sanarwar a jiya Asabar.

Osinbajo ya saka hannu a kan wasu sabbin muhimman dokoki 3

Osinbajo ya saka hannu a kan wasu sabbin muhimman dokoki 3

Sabbin dokokin da Akanbi ya lissafo sun hada;

1. Dokar Cibiyar Ma'ikata na babban birnin tarayya na shekarar 2018.

Cibiyar da za'a kafa karkashin wannan dokar zata rika daukan ma'aikata da kuma zartas da hukuncin ladabtarwa da ma'aikatan babban birnin tarayya da aka samu da laifi.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya yi ta'aziyyar rashin Kofi Annan

2. Dokar Kafa Hukumar Binciken Albarkatun Gandun Daji na Najeriya na shekarar 2018.

Wannan dokar zata bawa gwamnatin ikon kafa Cibiyar Binciken Gandun Daji da Najeriya wanda zata rika gudanar da bincike tare da koyarwa da bayar da horo a fannin binciken gandun daji.

Cibiyar zata samu rasa shida a kowanne yanki 6 dake Najeriya amma hedkwatan ta zai kasance a Ibadan.

3. Dokar kafa Makarantar Horas da masu gwaje-gwajen kiwon Lafiya da Fasaha dake Jos na shekarar 2018.

Wannan dokar zata bawa gwamnati ikon kafa Makarantar Horas da masu gwaje-gwajen kiwon Lafiya (Medical Laboratory Technology) inda za'a rika bayar da Diploma a fanoni daban-daban na Kimiyyar Binciken Kiwon Lafiya da wasu fanonin Kimiyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta-leko-ta-koma: Shugaba Buhari ya kwace Naira biliyan 14.9 din da ya ba wata jihar Arewa

Ta-leko-ta-koma: Shugaba Buhari ya kwace Naira biliyan 14.9 din da ya ba wata jihar Arewa

Ta-leko-ta-koma: Shugaba Buhari ya kwace Naira biliyan 14.9 din da ya ba wata jihar Arewa
NAIJ.com
Mailfire view pixel