Matsaloli 3 da Jam'iyyar PDP za ta fuskanta yayin Zaben fitar da 'Dan Takara

Matsaloli 3 da Jam'iyyar PDP za ta fuskanta yayin Zaben fitar da 'Dan Takara

Sharhin wani marubuci, Olusola Fabiyi, da jaridar The Punch ta wallafa a shafin ta ya bayyana cewa, akwai yiwuwar jam'iyyar adawa ta PDP ta fuskanci wasu matsaloli yayin fitar da dan takara na kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

Ko shakka ba bu guguwar siyasa na ci gaba da kadawa lunguna da sako na kasar nan yayin da babban zabe na 2019 ke ci gaba da karatowa, inda masu ruwa da tsaki kan harkokin siyasa ke kai komo wajen neman suna a fadin kasar nan.

Makonni kadan da suka gabata ne jiga-jigan 'yan siyasa da dama suka sauya sheka musamman ta ficewa daga jam'iyya mai ci ta APC zuwa PDP domin sauya salon taku na siyasa domin cimma manufofin su.

Wannan cincirindon na sauyin sheka ya kafa wani sabon tarihi a kasar nan da ba a taba fuskanta ba yayin da fiye da 'yan majalisa 50 na dokokin tarayyar Najeriya suka gudanar a tsakanin jam'iyyun siyasa daban-daban.

Matsaloli 3 da Jam'iyyar PDP za ta fuskanta yayin Zaben fitar da 'Dan Takara
Matsaloli 3 da Jam'iyyar PDP za ta fuskanta yayin Zaben fitar da 'Dan Takara

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai kalubalai da ka iya fuskantar jam'iyyar PDP yayin zaben fitar da gwani da zai fafata wajen neman kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

Ire-ren wannan matsaloli da kalubalai da marubuci Olusola ya yi sharhi a kai sun hadar da;

Yawan Manema Takara

Akwai jiga-jigan 'yan siyasa da suka shahara a kasar nan har guda 12 dake hankoron samun tikitin takarar kujerar shugaban kasa karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP da suka hadar da:

1. Tsohon Mataimakin Shugaban kasa kuma Turaki Adamawa, Atiku Abubakar.

2. Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki.

3. Tsohon Gwamnan jihar Kano, kuma Sanatan jihar ta Tsaki, Rabi'u Kwankwaso.

4. Gwamnan jihar Sakkwato kuma tsohon Kakakin Majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal.

5. Tsohon Gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Ahmed Makarfi.

6. Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo.

7. Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.

8. Wani fitaccen 'dan Kasuwa, Datti Baba-Ahmed.

9. Tsohon Ministan ayyuka na musamman, Tanimu Turaki.

10. Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa.

11. Tsohon Gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau.

12. Gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose

KARANTA KUMA: Wani Mahaukaci ya Kashe 'Dan tsubbu a jihar Anambra

Damuwa ta Fitar da 'dan Takara mafi cancanta

Jam'iyyar ta PDP ta na kuma fuskantar babban kalubale na fitar da dan takara da ka iya fafatawa a zaben 2019 dangane mashahuranci da kuma soyayyar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake zukatan al'ummar kasar nan.

Ko shakka ba bu jam'iyyar na fuskantar barzana ta fitar da dan takara mafi cancanta da ka iya lallasa shugaba Buhari da jam'iyyar sa ta APC yayin babban zabe.

Kudi da Dukiya ka iya tasiri ga 'yan Takara

Ana ci gaba da hasashen cewa kudi zai yi tasiri wajen fitar da dan takarar kujerar shugaban kasa kamar yadda marubuci Olusola ya bayyana.

Ba bu shakka doka ta jam'iyyar PDP ta kayyade cewa dole sai 'yan takarar sun biya kimanin N12m na sayen takardun takara na bayyana kudiri.

Sai dai wannan doka ta takaita ne kadai kan 'yan Takara Maza, inda dokar ta bayyana cewa Mata manema tikitin jam'iyyar za su biya N2m ne kacal na bayyana kudiri ba tare da biyan wani kudi na sayen takardun takara ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel