Gwamnatin Shugaba Buhari ta kware wajen yaudara - Atiku

Gwamnatin Shugaba Buhari ta kware wajen yaudara - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman tikitin takarar shugaban kasa tare da shugaba Muhammadu Buhari, Alhaji Atiku Abubakar ya ce tattalin arzikin kasar nan bai taba tabarbarewa ba kamar a lokacin nan na mulkin shugaba Buhari.

Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabin sa ga dubban magoya bayan jam'iyyar sa ta PDP a garin Enugu jiya lokacin da ya kai ziyarar sada zumunci.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta kware wajen yaudara - Atiku

Gwamnatin Shugaba Buhari ta kware wajen yaudara - Atiku

NAIJ.com ta samu cewa gwamnatin shugaba Buhari ba abunda ta iya sai yaudawa domin kuwa a sabanin samar da ayyukan yi miliyan uku da tayi alkawari duk shekara, yanzu ayyukan yi miliyan uku ne ake rasawa duk shekarar.

A wani labarin kuma, Yanzu haka dai mun samu cewa harkokin siyasa na cigaba da daukar zafi a jihar Ribas dake a kudu maso kudancin kasar nan bayan da labarin bude wani sabon ofishin jam'iyyar adawa a jihar ta All Progressives Congress (APC) a zagaye gari.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu mafusatan matasan da ake kyautata zaton masu goyon bayan bangaren jam'iyyar da Sanata Magnus Ngei yake jagoranta sun farwa dayan bangaren.

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duk wanda ya iya allon sa: Ban da ‘Dan takara a zaben 2019 –Makarfi

Duk wanda ya iya allon sa: Ban da ‘Dan takara a zaben 2019 –Makarfi

Duk wanda ya iya allon sa: Ban da ‘Dan takara a zaben 2019 –Makarfi
NAIJ.com
Mailfire view pixel