Har yanzu bamu wanke Saraki daga maganar Offa ba - Malami

Har yanzu bamu wanke Saraki daga maganar Offa ba - Malami

Abubakar Malami, Ministan Shari'a na kasa ya ce har yanzu ba'a wanke shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki daga zargin hannu cikin fashin Offa da akayi a jihar Kwara ba.

Malami da Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris sun karyata jita-jitar da ke yawo na cewa direktan PPP ya wanke Saraki daga zargin hannu cikin fashin Offa kamar yadda aka bayana a rahoton.

A rahoton da The Nation ta wallafa, Malami da Ibrahim sunyi tsokaci game da karar keta hakkin dan kasa da wasu suka shigar a madadin Bukola Saraki a wata babban kotun da ke Jabi a Abuja.

Har yanzu bamu wanke Saraki daga maganar Offa ba - IGP

Har yanzu bamu wanke Saraki daga maganar Offa ba - IGP

Anyi fashin Offa ne a ranar 5 ga watan Afrilu inda mutane 33 suka rasa rayuwansu ciki har da wata mace mai juna biyu da wasu jami'an yan sanda guda 12.

DUBA WANNAN: Kayi tsufa da mulkin Najeriya - Tambuwal ya fadawa Buhari

Hukumar 'yan sanda tayi ikirarin cewa Saraki da gwamnan jihar Kwara Abdulfatai Ahmed suna da hannu cikin fashin da akayi a Offa. Wasu daga cikin wadanda aka zargi da hannu cikin fashin sunyi ikirarin cewa Saraki ne yake daukan nauyinsu.

Sai dai Saraki da Abdulfatai sun musanta wannan zargin da ake musu.

Malami da Ibrahim sunce har yanzu ana cigaba da bincike saboda haka ba dai-dai bane a wanke Saraki da Abdulfatai daga hannu cikin fashin.

Malami ya ce har yanzu ana cigaba da binciken saboda haka ba dace a kammala cewa Saraki bashi da hannu cikin fashin. Ya kara da cewa muddin aka samu Saraki da hannu cikin fashin, kariyar da kundin tsarin mulki ta bashi ba zai tsiratar dashi ba.

A bangarensa, Saraki ya ce ana kokarin yi masa sharri ne kawai shi yasa ake kokarin tsoma hannunsa cikin fashin na Offa duk da cewa wadanda aka kama sun anbaci sunansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Babban buri na PDP ta lashe kowane zabe a 2019 - Inji Ahmad Makarfi

Babban buri na PDP ta lashe kowane zabe a 2019 - Inji Ahmad Makarfi

Duk wanda ya iya allon sa: Ban da ‘Dan takara a zaben 2019 –Makarfi
NAIJ.com
Mailfire view pixel