An gudanar da 'Kidayar adadin Awakai a 'Kasar Zambia

An gudanar da 'Kidayar adadin Awakai a 'Kasar Zambia

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito wani rahoto mai cike ban mamaki mun samu cewa, gwamnatin kasar Zambia dake yankin nahiyyar Afirka ta Kudu ta gudanar da kidayar adadin awakai daka fadin kasar.

'Kidayar da aka gudanar a shekarar 2017 da ta gabata ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta Zambia ta gano ce akwai adadin awakai 3, 476, 790 a fadin kasar kamar yadda jaridar Lusaka Times ta bayyana.

Hukumar fitar da kididdiga ta kasa tare da hadin gwiwar ma'aikatar kiwon Kifi da kuma Dabbobi na gida su ne suka dauki nauyin gudanar da wannan kidaya a shekarar 2017 da ta gabata.

An gudanar da 'Kidayar adadin Awakai a 'Kasar Zambia
An gudanar da 'Kidayar adadin Awakai a 'Kasar Zambia

Sakamakon wannan kidaya ya bayyana ne a yayin da kasar Zambia ta shiga kulla wata yarjejeniya da kasar Saudiya wajen sayar ma ta Awakai kimanin Miliyan guda a kowace shekara.

Kazalika kasar ta Saudiya tana kuma bukatar tumakai musamman raguna miliyan guda daga kasar Zambia a kowace shekara.

KARANTA KUMA: Osinbajo ya jagoranci Zaman Majalisar Tattalin Arziki

Legit.ng ta fahimci cewa, akwai damuwa dangane da wannan yarjejeniya ta ta yiwu ba za ta tabbata ba.

Kamar yadda shafin yanar gizo na Wikipedia ya bayyana, adadin Mutane dake kasar Zambia ba su wuci Miliyan 16.5 bayan kidayar da aka gudanar a shekarar 2016 da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel