Jerin masu neman takarar kujerar Shugaban kasa a PDP a 2019

Jerin masu neman takarar kujerar Shugaban kasa a PDP a 2019

Yayin da ake fara shirin zabe mai zuwa, mun fahimci cewa sama da mutane 10 ke nema su fito takarar kujerar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP a zaben na 2019. Mun kawo jerin wadannan ‘Yan takara wanda duk su ka fito daga Arewa.

Jerin masu neman takarar kujerar Shugaban kasa a PDP a 2019
Mutane da dama na neman tikitin PDP a zaben Shugaban kasa mai zuwa

1. Atiku Abubakar

2. Rabiu Kwankwaso

3. Ahmad Makarfi

4. Bukola Saraki

5. Aminu Tambuwal

6. Sule Lamido

7. Ibrahim Shekarau

8. Attahiru Bafarawa

9. Ibrahim Dankwambo

10. Kabiru Tanimu Turaki

Daga cikin ‘Yan takarar nan akwai irin su Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar wanda tun 1992 yake neman shugabancin kasar nan. Haka kuma akwai tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso cikin masu harin kujerar.

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki wanda ya bar APC kwanaki yace watakila ya nemi Shugaban kasa a 2019. Shi ma tsohon Shugaban Majalisar Wakilai kuma Gwamnan Sokoto a yanzu Aminu Tambuwal yace an matsa masa yayi takaran.

KU KARANTA: Wani rikakken Malami ya gano wanda zai lashe zaben 2019

Ba a nan abin ya tsaya ba, tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP kuma tsohon Gwamna Ahmad Muhammad Makarfi wanda ya dade yana dako a PDP zai sake jarraba sa’ar sa. Bayan shi ma akwai tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido yana harin tutar Jam'iyyar.

Tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau wanda ya taba takara a ANPP ya bayyana cewa tabbas zai sake neman Shugaban kasa a 2019 a PDP. Akwai kuma tsohon Gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa wanda ya taba takara a DPP a sahun ‘Yan takarar.

Gwamnan Jihar Gombe watau Ibrahim Hassan Dankwambo yana cikin masu neman tikitin PDP a zaben 2019. A karshe wani tsohon Ministan PDP watau Kabiru Tanimu Turaki yana cikin jerin wadanda ke neman samun tikitin Jam’iyyar PDP a zaben mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel