Akwai yiwuwar zan fito takarar shugaban kasa - Al-Mustapha

Akwai yiwuwar zan fito takarar shugaban kasa - Al-Mustapha

Hamza Al-Mustapha tsohon dogarin marigayi tsohon shugaban Najeriya na mukin soja, Janar Sani Abacha, ya ce a shirye yake ya fito takarar shugabancin kasa a zaben shekarar 2019 muddin jama'ar Najeriya sun bukaci ya fito.

Manjo Al-Mustapha (murabus) ya yi bayyana haka ne a jiya Laraba a wata hira da ya yi da manema labarai a Kaduna jim kadan bayan ya kammala taro da 'yan kungiyar United Christian Leaders Eagle Eye Forum da suka nemi ya fito takarar.

Akwai yiwuwar zan fito takarar shugaban kasa - Al-Mustapha
Akwai yiwuwar zan fito takarar shugaban kasa - Al-Mustapha

"Ba zan furta cewa zan fito takarar shugabancin kasa ba amma idan jama'a sun bukaci inyi hakan, wannan kuma zabinsu ne.

"Ni ba mutum bane mai kwadayin mulki, idan da ina da kwadayi da tuni gwarjini na ta dushe amma idan jama'a sun bukaci in fito, zan amsa kirarsu," inji shi.

DUBA WANNAN: Zamu bijrewa duk wani yunkuri na tsige Saraki - Dan majalisa

A cewarsa, abinda ya sanya a gaba shine kare hakkin 'yan Najeriya kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Al-Mustapha ya yi tsokaci kan lamarin tsaro a Najeriya inda ya shawarci gwamnati ta sake dawo da shigen bincike saboda suna da amfani wajen gano bata gari dake safarar makamai zuwa Najeriya.

Ya kuma yi kira da cewa ya kamata a yiwa dokar rundunar 'yan sanda garambawul ta yadda za'a karfafa ayyukan 'yan sanda musamman a karkara a sassan kasar.

Da yake tsokaci kan ayyukan hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati EFCC, ya misalta hukamar da "karamin birri da aka bawa igiya domin ya kama giwa amma ya yi watsi da aikinsa ya koma yana barna a dajin.

"Idan kana son magance rashawa, dole ka bullo masa ta fuskoki daban-daban; EFCC bata da karfin da zata yaki rashawa a Najeriya.

"Hukumar na bukatar karin karfi da ma'aikata ta yadda zata rika yin musayar bayanai da hukumomin tsaro na kasashen ketare domin kwato kudade da aka boye a kasashen tare da hukunta wadanda aka samu da laifi."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel