Rai bakon Duniya: Kananan yara yan makaranta 22 sun nutse a babban Tekun Nilu

Rai bakon Duniya: Kananan yara yan makaranta 22 sun nutse a babban Tekun Nilu

- Dalibai 22 sun gamu da ajalinsu a sakamakon hadarin Teku

- Daliban sun gamu da ajalin ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Makaranta

Akalla kananan yara yan makaranta su ashirin da biyu ne suka gamu da ajalinsu a sakamakon jirkicewar kwale-kwalen dake dauke dasu yayi a cikin Tekun Nilu a yayin da suke kan hanyarzu ta zuwa makarantar, inji rahoton kamfanin dillancin labaru.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a kasar Sudan, inda kwale kwalen dake dauke da daliban ya jirkice, sa’annan ya nutse, wanda hakan yayi sanadin rasa rayukan dalibai 22 daga cikin dalibai 40 dake cikinta.

KU KARANTA: Hajji ibadar Allah: Gwamnatin kasar Birtaniya ta tura Sojojinta don gabatar da aikin Hajji

Haka zalika baya ga daliban, akwai wata babbar Mata data rasu a sakamakon hadarin Tekun, wanda ya faru a sakamakon mamakon ruwan sama da ya sauka, wanda yayi sanadin ambaliyan ruwa cikin kwale kwalen, daga nan ya nutsa.

Zuwa yanzu dai hukumomi a kasar Sudan na ta kokarin neman gawarwakin mamatan a daidai inda hatsarin ya faru a cikin tafkin Nilu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel