Obasanjo na daya daga cikin kalubalen da muke fuskanta a Najeriya - Tinubu

Obasanjo na daya daga cikin kalubalen da muke fuskanta a Najeriya - Tinubu

A ranar Talatar da ta gabata ne tsohon gwamnan jihar Legas kuma Kanwa Uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya fedewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo Biri har wutsiya dangane da halin da kasar nan ke ciki a yanzu.

Tsohon gwamnan ya zargi Obasanjo da haddasa duk wani kalubale da kasar Najeriya ke fuskanta a halin yanzu sakamakon dashen mummunan tushe da ya yi a yayin da yake shugabancin kasar nan a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, tsohon gwamnan ya na kuma kyautata zato tare da cikakken aminci dangane da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta lashe zaben 2019.

Tinubu yayi wannan furuci ne yayin ganawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar sa ta Legas kamar yadda rahotanni suka bayyana, inda yake cewa tuni shugaba Buhari ya haskaka kansa a matsayin jagora na gari duba da kalubalen da gwamnatin sa ke fuskanta.

Obasanjo na daya daga cikin kalubalen da muke fuskanta a Najeriya - Tinubu
Obasanjo na daya daga cikin kalubalen da muke fuskanta a Najeriya - Tinubu

Shugaban na jam'iyyar APC ya kuma yi tir dangane da yadda Obasanjo ke yawaita suka gami da caccakar gwamnatin shugaba Buhari, da a cewar sa hakan ba zai hana 'yan Najeriya sake cincirindon kada ma sa kuri'u su ba a zaben 2019.

Ya ci gaba da cewa, katsalandan din da tsohon shugaban ke yi kan al'amurran kasar ba za su wanke illar da ya haddasa yayin da yake shugabancin kasar nan shekaru fiye da goma da suka gabata.

KARANTA KUMA: An yi na farko an yi na karshe: Ba zan sake barin PDP ba ko me zai faru Inji Atiku

Tinubu ya kuma bayyana farin cikin sa dangane da nasarar da jam'iyyar APC yayin zabukan maye gurbi da aka gudanar cikin jihohin Katsina, Bauchi, da kuma Kogi a karshen makon da ya gabata.

Kazalika ya kuma yabawa shugaban jam'iyyar na kasa, Mista Adams Oshiohole, dangane da yadda yake jagorantar jam'iyyar wajen kwankwadar romon dimokuradiyya.

Ya kuma kwadaitar da al'ummar kasar akan su tabbata sun mallakin katin zaben domin kuwa shi ne makamin su na fafata yaki a yayin zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel