Buhari ya shafe kwanaki fiye da 170 a kasar waje daga 2015 zuwa yanzu

Buhari ya shafe kwanaki fiye da 170 a kasar waje daga 2015 zuwa yanzu

Mun fahimci cewa a halin yanzu Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zama Shugaban kasar da ya fi kowane yawan kwanakin jinya a Kasar waje. Shugaba Buhari ya shafe kwanaki sama da 170 a Kasar wajen daga hawan sa mulki.

Buhari ya shafe kwanaki fiye da 170 a kasar waje daga 2015 zuwa yanzu
Buhari ya fi kowane Shugaba Kasa zuwa ganin Likita

A Yunin 2016 ne Shugaba Buhari ya fara fita waje domin ganin Likita, a wancan lokaci Shugaban yayi alkawarin yin kwanaki 10 domin a duba cutar da ke damun sa a kunne, sai dai Buhari ya shafe kwanaki 14 kafin ya dawo Najeriya.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna Bafarawa yace ba zai bar Jam'iyyar PDP ba

Tsakanin Yunim 2016 zuwa Agustan 2017, Shugaba Buhari ya garzaya Birnin Landan sau 3 inda ya nemi a duba lafiyar sa. A cikin wannan lokaci, Buhari ya shafe kwanaki 168 ba ya Najeriya inji cibiyar ICiR mai bin kwa-kwaf a Duniya.

Marigayi Shugaba Ummaru Yaradua ne yayi kwanaki kusan 109 a kasar waje yana jinya a lokacin yana mulki. Gaba daya dai ‘Yaradua bai kai shekaru 3 a kan mulki ba ya bar Duniya. Yanzu kwanakin da Buhari ya shafe sun zarce hakan.

A tsakiyar Mayu ma dai jirgin Buhari ya tsaya a Landan inda ake zargin Likita ya gani. Yanzu haka dai Shugaban na Najeriya yana Landan inda yake hutawa. Akwai lokacin da Buhari ya samu kyakkayawar tarba bayan ya shafe kwanaki a Turai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel