Rana zafi: Mataimakin Kaakakin majalisar dokokin jihar Kaduna ya yi murabus

Rana zafi: Mataimakin Kaakakin majalisar dokokin jihar Kaduna ya yi murabus

Mataimakin Kaakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, John Kwaturu ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda sakamakon yin murabus da yayi daga mukaminsa sakamakon ficewarsa daga jam’iyyar APC ya koma jam’iyyar PDP.

Majiyar NAIJ.com ta ruwato Kwaturu ne wakilin karamar hukumar Kachia a majalisar dokokin jihar Kaduna ya fice daga APC ne a ranar Asabar, 11 ga watan Agusta, inda ya sheke zuwa PDP.

KU KARANTA: Babban sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo

Rana zafi: Mataimakin Kaakakin majalisar dokokin jihar Kaduna ya yi murabus

Kwaturu

Kwaturu ya danganta ficewarsa daga APC bisa rashin iya gudanar da ingantaccen mulki a Kaduna, kekketa doka kaca kaca da kuma rabuwar kai da ake fama da shi a jam’iyyar.

Bugu da kari Kwaturu yace ya yanke shawarar yin murabus daga mukaminsa ne bayan tattaunawa da abokan siyasarsa da kuma shuwagabannin al’umma da kuma jama’an mazabarsa.

Daga karshe Kwaturu ya bayyana godiyarsa ga gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da sauran yayan majalisar dokokin jihar Kaduna bisa goyon bayan da suka ba shi wajen gudanar da aikinsa a tsawon shekaru uku da yayi kwashe akan mukamin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hadimin Oshiomhole da dumbin magoya bayansa sun fita daga APC, sun fadi dalili

Hadimin Oshiomhole da dumbin magoya bayansa sun fita daga APC, sun fadi dalili

Hadimin Oshiomhole da dumbin magoya bayansa sun fita daga APC, sun fadi dalili
NAIJ.com
Mailfire view pixel