Gawon shanu: Wata tsohuwa ta fadi some a filin jirgi wajen tarbar Atiku

Gawon shanu: Wata tsohuwa ta fadi some a filin jirgi wajen tarbar Atiku

Wata tsohuwa mai suna Grace Osagie kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu ance wai ta fadi a some a filin jirgin kasa da kasa na jihar Benin inda taje domin tarbar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar.

Kamar dai yadda wani ganau ya shaidawa majiyar mu, yace ana kyautata zaton tsabar zafin rana ne ya sa matar suma biyo bayan cincirindon magoya bayan fitaccen dan siyasar da suka je tarbar sa.

Gawon shanu: Wata tsohuwa ta fadi some a filin jirgi wajen tarbar Atiku

Gawon shanu: Wata tsohuwa ta fadi some a filin jirgi wajen tarbar Atiku

KU KARANTA: Yan sandan Najeriya sun cafke farfesan bogi

NAIJ.com ta samu cewa a nan take ne dai jama'a suka taru kan tsohuwar inda kuma suka garzaya da ita asibitin dake kusa domin nemar mata lafiya.

A wani labarin kuma, Da safiyar yau ne dai aka tashi da wani labari a wata jarida dake a Najeriya da ke cewa kasashen duniya da dama ciki kuwa hadda Amurka, Saudiyya da ma tarayyar kasashen turai suna cigaba da matsin lamba ga Shugaba Buhari kada ya nemi takarar tazarce a 2019.

To sai dai tuni fadar shugaban kasar ta fito ta karyata batun ta bakin mai taimakawa shugaban kasar ta hanyar sadarwa, Malam Garba Shehu wanda yace labarin kazon kurege ne kawai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jam’iyyar APC ta jahar Filato ta tabbatar da Buhari a matsayin dan takararta

Takarar shugaban kasa: APC ta jahar Filato ta bayyana goyon bayanta ga Buhari

Jam’iyyar APC ta jahar Filato ta tabbatar da Buhari a matsayin dan takararta
NAIJ.com
Mailfire view pixel