Sarkin Musulmi ya bayyana babban musabbabin mutuwar aure a tsakanin Musulmai

Sarkin Musulmi ya bayyana babban musabbabin mutuwar aure a tsakanin Musulmai

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana bacin ransa game da yawaitar mutuwar aure a tsakanin Musulmai, inda yace lamarin ya janyo muwahara a tsakanin jama’a saboda matsalar da yake haifarwa ga iyalai, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Sultan ya bayyana haka ne a yayin taron Malamai da hukumar Zakka da wakafi ta jihar Sakkwato ta shirya, inda yace mutuwar aure na biyo bayan almubazzarancin da ake yi a yayin bukukuwa ne.

KU KARANTA: Yan kunar bakin wake sun sabbaba mutuwar mutane 10 a Madagali

“Ya dace Malamanmu su ilimantar da jama’a game da almubazzaranci a yayin bukukuwan aure, saboda hakan na haifar da rudani dake sanadin mace macen aure a tsakanin ma’aurata.” Inji shi.

Sultan yayi kira ga Malamai dasu tabbata sun ji tsoron Allah a dukkanin ayyukansu, hakan zai samar da kyawawan halaye a tsakanin al’umma, haka zalika yayi kira ga Attajirai dasu daure su dinga taimaka ma gajiyayyu, don rage radadin halin da ake ciki.

A nasa jawabin, shugaban hukumar, Lawal Maidoki ya jinjina ma Malaman, tare da jaddada godiyarsa garesu bisa gudunmuwar da suke baiwa hukumar wajen samu nasarorinta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duk wanda ya iya allon sa: Ban da ‘Dan takara a zaben 2019 –Makarfi

Babban buri na PDP ta lashe kowane zabe a 2019 - Inji Ahmad Makarfi

Duk wanda ya iya allon sa: Ban da ‘Dan takara a zaben 2019 –Makarfi
NAIJ.com
Mailfire view pixel