2019: 'Yan jam'iyyar PDP 500 sun rungumi tsintsiya a jihar Jigawa

2019: 'Yan jam'iyyar PDP 500 sun rungumi tsintsiya a jihar Jigawa

Mambobin jam'iyyar PDP fiye da 500 ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a karamar hukumar Roni dake Jihar Jigawa.

Ciyaman din jam'iyyar APC na jihar, Alhaji Ado Sani Kiri, wanda ya samu wakilcin jigo a jam'iyyar, Alhaji Abdullahi H. Gumel ne ya tarbi sabbin mambobin inda ya yi alkawarin jam'iyyar zata basu kulawa kamar yadda ake bawa kowa.

A cewarsa, babu bambanci tsakanin sabbin mambobi da tsaffi a jam'iyyar, abinda ke da muhimmanci shine irin biyaya da da'a da mutum ke yiwa dokoki jam'iyya da bayar da gundunmawa wajen cimma manufofin jam'iyyar.

2019: 'Yan jam'iyyar PDP 500 sun rungumi tsintsiya a jihar Jigawa
2019: 'Yan jam'iyyar PDP 500 sun rungumi tsintsiya a jihar Jigawa

DUBA WANNAN: Ambaliyar ruwa ta tagayyara mutane, ta lalata gidaje fiye da 50 a jihar Kebbi

A jawabin da ya yi a wajen taron, wani dan takarar majalisa na yankin Kazaure/Roni/Yankwashi/Gwiwa, Alhaji Kabiru Mohammed Roni, ya jinjinawa sabbin mambobin kan yadda suka jefar da jam'iyyar da bata kishin 'yan Najeriya suka dawo APC.

Alhaji Kabiru wanda ya taka rawar gani wajen zawarcin sabbin mambobin ya yi alkawarin aiki tare da su domin ganin jam'iyyar tayi nasara a jihar da ma kasa baki daya.

A yayin da yake magana a madadin sabbin mambobin da suka fito daga gundumomi bakwai na karamar hukumar Roni, Malam Isa Naradi, yace sun dawo jam'iyyar APC ne saboda irin shugabanci na gari da Gwamna Muhammadu Badaru keyi a jihar.

Ya kuma yi alkawarin goyon bayan takarar Alhaji Kabiru Muhammad wanda ya ce mutum ne mai rikon amana da karamci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel