Ku daina aron kudi domin yanka ragon layya – Kungiyar kare hakkin Musulmi

Ku daina aron kudi domin yanka ragon layya – Kungiyar kare hakkin Musulmi

Kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta hannun daraktan ta, Farfesa Ishaq Akintola ta gargadi Musulmai da kada su kuskura su kai ga aron kudi don kawai su yanka ragon layya a lokacin bikin babban sallah da za’ayi a ranar 21 ga watan Agusta.

Kungiyar tace addinin Islama bata yarda da mutun ya takura kansa don kawai yayi bikin addini ba.

Ta kuma bukaci Musulmai da suyi daidai ruwa daidai tsaki ma’ana su lura da karfin aljihunsu wajen kashe kudade a bikin sallan.

Ku daina aron kudi domin yanka ragon layya – Kungiyar kare hakkin Musulmi
Ku daina aron kudi domin yanka ragon layya – Kungiyar kare hakkin Musulmi

A cewar ta addinin Musulunci saukakkakiya ce, kuma Allah bai takurawa kowa akan abunda baida karfin yi ba.

KU KARANTA KUMA: Hukumar INEC ta bayar da takardun shaidar dawowa ga zababbun sanatoci

Haka zalika kungiyar ta jadadda cewa layya kamar aikin hajji ne wajibi ne amma ga mai iko.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel