Idon EFCC ya hango wasu makudan kudaden jihar Akwa Ibom a asusunsu wasu lauyoyi

Idon EFCC ya hango wasu makudan kudaden jihar Akwa Ibom a asusunsu wasu lauyoyi

- Bayan bankado asirin yadda wasu makudan Nairori suke shinfide a asusun wasu, EFCC ta gayyace su

- Sai babu wanda ya amsa gorin gayyatar da ta yi musu

- Wadanda ake zargin kudaden a asusunsu na banki sun hada manyan lauyoyi a jihar Akwa Ibom

Idon EFCC ya hango wasu makudan kudaden jihar Akwa Ibom a asusunsu wasu lauyoyi

Hukumar EFCC ta bi kadin wasu makudan kudade sama da Naira N1.4b mallakin jihar Akwa Ibom da take zargin sun shiga wasu asusun banki guda 11.

Idon EFCC ya hango wasu makudan kudaden jihar Akwa Ibom a asusunsu wasu lauyoyi
Idon EFCC ya hango wasu makudan kudaden jihar Akwa Ibom a asusunsu wasu lauyoyi

Ana dai zargin asusun bankin da ake zargin kudin sun shiga mallakin wasu fitattun lauyoyi ne da ke kasar nan. Kuma hukumar na gab da fara tuhumarsu.

Daya daga cikin lauyoyin da ake zargi ya rubutawa hukumar ta EFCC yadda aka yi har kudin suka shigo asusun bankinsa, ya ce kudin ladan aikinsa ne da ya yiwa gwamnatin jihar ta Akwa Ibom kan wasu aiyuka 16.

Ya kara da cewa babu wata rubutacciyar shaida da zai iya gabatarwa wacce zata nuna wannan yarjejeniya tsakaninsa da gwamnatin jihar.

Jami'an hukumar ta EFCC sun bayyana cewa biyan kudin da aka yi cikin asusu 11 ya saba doka, domin a ka'ida za'a iya biya ne ta hanyar cakin kudi ba turawa ba.

KU KARANTA: Tun kafin ai nisa EFCC ta fara bincikar Fayose da matarsa

Kawo yanzu dai hukumar ta EFCC ta gayyato wasu jami'an gwamnatin jihar ta Akwa Ibom, wadanda suka hadar da Kwamishinan kudi Nsikan Linus da babban sakataren gwamnatin jihar da Daraktan kudi na ma'aikatar Shari'a tare da mataimakin babban akawun jihar Mfon Jacobson Udomah.

Haka zalika hukumar ta EFCC ta yi korafin cewa tun a ranar 19 ga watan Yulin da ya gabata ne jami'ansu suka isa babban birnin jihar ta Akwa Ibom wato Uyo, inda suka mika goron gayyata ga wadanda ake zargin, amma babu wanda ya amsa gayyatar tasu.

Har wa yau, hukumar ta bayyana samun wata takarda wadda sakataren gwamnatin jihar da atoni janar da kuma kwamishinan sharia na jihar suka aike tare da tabbacin cewar wanda ake bukatar su bayyana a ofishin hukumar na EFCC zasu bayyana duk da cewa sun ki amsa gayyatar da aka musu tun farko.

“Atoni-janar da kansa ya ziyarci ofishinmu dake Abuja domin bamu tabbacin cewa zai kawo wadanda ake bukatar yiwa tambayoyi da kansa, amma shiru kake ji kamar an shuka dusa, amma muna jadadda musu cewa lallai ne sai sun amsa goron wannan gayyata da akai musu” inji hukumar ta EFCC.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel