Manyan aiyuka 6 da shugaba Buhari ya yi a kowanne yankin Najeriya

Manyan aiyuka 6 da shugaba Buhari ya yi a kowanne yankin Najeriya

A yayin da zaben 2019 ke karatawo, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta fitar da wasu muhimman aiyuka shida da tayi a kowanne yankunan Najeriya da zasu kawo cigaba ga rayuwan al'ummar yankunan.

Manyan aiyuka 6 da shugaba Buhari ya yi a kowanne yankin Najeriya
Manyan aiyuka 6 da shugaba Buhari ya yi a kowanne yankin Najeriya

1. Lagos Ibadan express road (Kudu maso Yamma)

Babban titin Legas zuwa Ibadan yana daya daga cikin aiyukan da gwamnatocin baya suka dade suna ikirarin zasu yiwa gyara tare da fadadawa sai dai a yanzu gwamnatin shugaba Buhari ta tasar wa aikin gadan-gandan.

A wata rahota da Daily Trust ta wallafa, gwamnatin tarayya ta ware N64 biliyan don karasa wata bangare na aikin.

Ministan makamashi, aiyuka da gidaje, Babatunda Fashola yace gwamnati ta amince da ware kudin ne saboda muhimmancin da hanyar keda shi ga matafiya.

2. Babban titin Kano zuwa Maiduguri (Arewa maso Gabas/Arewa maso Yamma)

Babban titin Kano zuwa Maiduguri tana daya daga cikin manyan aiyukan titi da gwamnatin shugaba Buhari ta fara gudarwa da kudin Sukuk. Ministan Makamashi, ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola yace gwamnati ta mayar da hankali kan ayyukan ne saboda cika wa al'umma akawuran da aka dauka yayin yakin neman zabe.

DUBA WANNAN: Canji: Ma’aikatar gwamnatin tarayya ta mayar da biliyan N3bn aljihun gwamnati

3. East-West Road (Kudu maso Kudu/Kudu maso Gabas)

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi yace 'yan kwangilar dake aikin titin na bukatar N100 biliyan domin kammala gyra da fadada titin.

Mr Ameachi tare da Ministan Neja-Delta, Uguru Usani sun fadi hakan ne yayin da suka kai ziyarar duba aikin da aka fara da Warri zuwa Eleme Junction kamar yadda Premium Times ta wallafa.

4. Jami'ar Maritime ta Jihar Delta (Kudu maso Kudu)

An kafa wannan jami'ar ne ta musamman saboda koyar da darussa masu alaka albarkatun ruwa. Tuni jami'ar ta fara daukan dalibai masu karatun digiri a sassa daban da suka hada da karatun Injiniya da sauransu.

5. Jiragen Kasa na zamani (Babban birnin tarayya Abuja)

An bayar da kwangilar gina tasha da saya jiragen kasar ne tun watan Mayu na 2007 a zamanin mulkin shugaba Olusegun Obasanjo sai an dakatar da aikin saboda rashin kudi.

Gwamnatin shugaba Buhari ta farfado da aikin inda ta bayyana cewa an kammala shimfida titin jirgin da kuma tashoshi 12 a yayinda ake cigaba da karasa sauran ayyukan.

6. Kamfanin Karafa ta Ajaokuta (Arewa ta tsakiya)

A yunkurinta na farfado da masana'antu da kamfanoni da suka dade basu tabbuka wani abin azo a gani, gwamnatin shugaba Buhari ta ware mukuden kudade don gyaran kamfanin karafar dake jihar Kogi.

7. N Power

N power shiri ne wadda gwamnatin shugaba Buhari ta bullo dashi saboda bawa matasa horo kan sana'o'i daban-daban ta yadda zasu kasance masu dogaro da kansu kana a rage matsalar rashin aiyukan yi da ake fama dashi a kasar.

A karkashin shirin ana koyar da matasa sana'o'i kamar aikin noma da kiwo, aikin malanta, kiwon lafiya da sauransu na tsawon shekaru biyu kafin a yaye su domin su cigaba da sana'oin da suka koya.

Wannan shiri ya karede dukkan jihohi 36 da na kasar har ma da babban birnin tarayya Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel