Mu na alfahari da goyon bayan ka akan 'Dan mu, Buhari - Sarkin Daura ga Osinbajo

Mu na alfahari da goyon bayan ka akan 'Dan mu, Buhari - Sarkin Daura ga Osinbajo

Sarkin garin Daura dake jihar Katsina, Alhaji Umar Faruk, ya bayyana godiyarsa ga mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinabjo, da cewar su na alfahari dangane da goyon bayan sa akan ɗan su, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wajen jagorantar kasar zuwa ga ci gaba da bunkasa.

Cikin wata sanarwa ta Kakakin mataimakin shugaban kasa, Mista Laolu Akande, ya bayyanacewa Sarkin Daura ya yi wannan furuci yayin da Ubangidan sa ya kai ziyarar ban girma fadar sa a ranar Alhamis din da ta gabata.

Laolu ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata da cewar Sarkin ya bayyana godiyar sa tare da yabawa Osinbajo dangane da goyon bayan shugaba Buhari wanda ɗa ne ga masauratar.

Mu na alfahari da goyon bayan ka akan 'Dan mu, Buhari - Sarkin Daura ga Osinbajo
Mu na alfahari da goyon bayan ka akan 'Dan mu, Buhari - Sarkin Daura ga Osinbajo

Legit.ng ta fahimci cewa, Sarkin na Daura ya yabawa mataimakin shugaban kasar sakamakon amincewar sa gami da tsayuwar daka wajen goyon bayan shugaba Buhari tare da taka muhimmiyar rawa ta gani wajen gudanar da shugabancin kasar nan.

KARANTA KUMA: Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki na jihar Kaduna ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Sarkin yake cewa, a tarihi ba a taba samun makamancin wannan gwamnati ba inda hadin kai a tsakanin shugaban kasa da mataimakin sa ke aiki tukuru bisa tsari na fahimta da kuma rikon amanar juna.

Ya kara da cewa, gwamnatin tun kafuwarta ta bayyana irin amincin ta gami da nagarta inda ko shakka babu darajar shugaba Buhari da mataimakin sa ta wuce misali.

Kazalika, Sarkin ya mika godiyar sa ga gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, dangane da rawar da gwamnatin sa ke takawa wajen kawo ci gaba da kuma inganci cikin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel