Da dumin sa: Jirgi mai saukar angulu yayi hatsari da mutane 9 a cikin sa

Da dumin sa: Jirgi mai saukar angulu yayi hatsari da mutane 9 a cikin sa

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa ba da dadewa ne ba dai waji jirgi mai saukar angulu kirar helikwafta ya rikito da mutum tara a cikin sa a wasu tsaunuka dake can a kasar Japan.

Hotunan farko farko dai da wata tashar yada labaran kasar ta fitar sun nuna buraguzan jirgin a cikin itace a garin Gunma dake a arewa maso yammacin garin Tokyo, babban birnin kasar.

Da dumin sa: Jirgi mai saukar angulu yayi hatsari da mutane 9 a cikin sa
Da dumin sa: Jirgi mai saukar angulu yayi hatsari da mutane 9 a cikin sa

KU KARANTA: Yan kwankwasiyya sama da dubu dari 5 sun koma PDP a Edo

Legit.ng ta samu haka zalika cewa jirgin dai kirar Bell 412 ya bar filin saukar sa ne a safiyar yau da nufin zuwa koyar da mutanen ciki.

A wani labarin kuma, Akalla mahajjata takwas ne kamar yadda muka samu daga majiyar ta kamfanin dillacin labarai da suka fito daga jihar Kebbi dake a Arewa maso yammacin Najeriya sukayi kicibis da 'yan damfara a kasar Saudiyya.

Haka zalika kamar yadda muka samu, 'yan damfarar sun yiwa mahajjatan wayau inda har suka samu nasarar kwace masu dukkan kudaden guzurin su sannan suka yi layar zana.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel