Da wuya idan ba nine zan fara zama shugaban kasa a yan Igbo ba - Okorocha

Da wuya idan ba nine zan fara zama shugaban kasa a yan Igbo ba - Okorocha

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha a ranar Alhamis, 9 ga watan Agusta ta bayyana cewa da wuya idan ba shine zai zamo shugaban kasa na farko daga kabilar Igbo ba.

Gwamnan na jihar Imo, yayi Magana ne a lokacin wani taron kalaci da manema labarai a gidan gwamnati, cewa yafi sauran yan siyasan Igbo tarin masoya ba wai a kudu kadai ba.

Sai dai Okorocha ya bayyana abunda ke ci masa tuwo a kwarya tsakanin shugabannin Igbo, inda yace “abun bakin ciki ne yadda yan Igbo basa daukaka nasu, sai dai yadda zasu rusa nasu da hannunsu."

Da wuya idan ba nine zan fara zama shugaban kasa a yan Igbo ba - Okorocha
Da wuya idan ba nine zan fara zama shugaban kasa a yan Igbo ba - Okorocha
Asali: Depositphotos

Ya kuma bayyana cewa ba zai dogara da goyon bayan yan Igbo ba wajen cimma burinsa na zama shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: An saki Lawal Daura, amma an kwace masa fasfo

Kan sake takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan yace yan kabilar Igbo sun shirya marawa Buhari baya dari bisa dari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel