Buhari ya aiko da sako ga wasu dattijan arewa 2 a karon farko tun bayan tafiyar sa Ingila

Buhari ya aiko da sako ga wasu dattijan arewa 2 a karon farko tun bayan tafiyar sa Ingila

A yau, Alhamis, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiko da sakon taya murna ga tsohon gwamnan jihar Filato, Manjo Janar Lawrence Onoja (mai ritaya), day a cika shekara 70 a duniya.

Kazalika ya aike da wani sakon ga ambasada Abdullahi Atta, wanda ya cika shekara 90 a duniya a ranar juma’a da ta gabata.

A jerin sakonnin da mai taimakawa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, Femi Adesina, ya saki, shugaba Buhari ya taya iyali da abokan Onoja murnar ganin wannan rana ta zagayowar ranar haihuwar sa.

Buhari ya aiko da sako ga wasu dattijan arewa 2 a karon farko tun bayan tafiyar sa Ingila

Buhari

Buhari ya yi waiwaye a kan irin aiki tukuru, kishin kasa da riko da gaskiya da Onoja ya yi lokacin da yake da yake rike da mukamai a hukumar soji da kuma lokacin day a zama gwamna a jihohin Najeriya biyu.

A wani sakon na daban da Malam Garba Shehu, babban mai taimakawa shugaban kasa a bangaren yada labarai ya saki, Buhari ya taya Ambasada Attah murnar cika shekaru 90 a duniya.

DUBA WANNAN: Wani dan Najeriya ya yi murnar cika shekaru 100 a gidan yari (Hoto)

A cikin sakon, shugaba Buhari ya bayyana yadda Ambasada Attah ya nuna halin dattako da kishin kasa lokacin da yake aikin gwamnati da kuma lokacin day a kasance jakadan Najeriya a kasashen ketare.

Shugaba Buhari ya yiwa dattijan biyu addu’ar samun Karin koshin lafiya da kuma zama abun koyi ga matasa dake da burin hidimtawa najeriya domin kishin kasa ba don biyan bukatar kansu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wani Gwamna daga Arewacin Najeriya ya koka kan yadda EFCC ke takura masa da mukarrabansa

Wani Gwamna daga Arewacin Najeriya ya koka kan yadda EFCC ke takura masa da mukarrabansa

Wani Gwamna daga Arewacin Najeriya ya koka kan yadda EFCC ke takura masa da mukarrabansa
NAIJ.com
Mailfire view pixel