Ibrahim Magu ya taso Lawal Daura a gaba bisa zargin satar wasu kudi

Ibrahim Magu ya taso Lawal Daura a gaba bisa zargin satar wasu kudi

Mun samu labari cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na neman taso tsohon Shugaban DSS watau Lawal Daura da aka tsige daga ofishin sa a makon nan a gaba bisa zargin batar da wasu kudi.

Ibrahim Magu ya taso Lawal Daura a gaba bisa zargin satar wasu kudi
Ana zargin Daura da yin awon-gaba da kudin da aka bar wa DSS

Hukumar EFCC na neman soma bincike kan wasu kudi har sama da Naira Biliyan 17 da ake zargin tsohon Shugaban DSS Daura yayi sama da fadi da su lokacin yana ofis. Yanzu har EFCC ta kai wa Daura ziyara a inda yake tsare.

Idan ba ku manta ba, bayan an sallami Lawal Daura daga aiki, Jami’an ‘Yan Sanda sun tsare sa, har yanzu dai tsohon Shugaban na DSS yana amsa tambayoyi a ofishin ‘Yan Sandan Kasar da ke Unguwar Guzape a cikin Garin Abuja

Ana sa rai bayan an gama yi wa Daura tambayoyi a mika sa gaban EFCC domin jin inda ya kai wasu kudin Hukumar ta DSS. Tsohon Shugaban DSS ya bar wa Daura gadon wasu Biliyoyin Dalolin kudi da yanzu an neme su an rasa.

KU KARANTA: Filla-fillar yadda Osinbajo ya tsige Lawal Daura kuma ya sa aka daure shi

Ita Ekpeyong wanda ya rike DSS kafin zuwan Lawal Daura ya karbi wasu kudi har Naira Biliyan 20 a lokacin mulkin Jonathan, Ekpeyong ya bar kusan Biliyan 17 bayan ya bar ofis wanda ake zargin yanzu Lawal Daura ya handame su.

An gano da batun wannan kudi ne a lokacin da ake binciken badakalar da aka tafka a Hukumar NIA. Lawal Daura ne dai ya hana EFCC ta kama tsohon Shugaban DSS Ita Ekpeyong da kuma Ayo Oke na Hukumar NIA a wancan lokacin.

Idan ba ku manta ba dai Shugaban DSS na kasar ne ya aika takarda Majalisa inda ya hana a tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban Hukumar EFCC. Kun san cewa an nada Matthew Seiyefa a matsayin wanda zai rike DSS na rikon kwarya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel