Jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta gargadi 'yan takarar Gwamna 11 akan kai hari ga 'Yan adawa

Jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta gargadi 'yan takarar Gwamna 11 akan kai hari ga 'Yan adawa

Jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna, ta gargadi 'yan takara masu hankoron kujerar gwamnatin jihar akan kai hare-hare da yada gora a tsakanin su da abokanan adawar su domin neman samun amincewar wakilan jam'iyyar.

Shugaban jam'iyyar, Mista Hassan Hyat, shine ya yi wannan jan kunne yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Jos a ranar Talata ta yau, inda ya gargadin 'yan takarar akan caccakar abokanan su na adawa.

Ya shawarci masu hankoron kujerar gwamnan jihar akan su mayar da hankali wajen yadda suka nufaci dawo da malaman makaranta da sauran ma'aikata da gwamnan jihar ya sallama daga bakin aiki tare da toshe hanyar su ta samun abinci.

Shugaban Jam'iyyar PDP na kasa; Prince Uche Secondus
Shugaban Jam'iyyar PDP na kasa; Prince Uche Secondus
Asali: Depositphotos

A madadin sukar abokanan su na adawa, shugaban jam'iyyar ya nemi manema takarar akan su bayyana akidar su dangane da yadda za su inganta harkokin da suka shafi lafiya, noma, ilimi da kuma tituna a jihar ta Kaduna.

Kazalika Mista Hyat ya nemi manema takarar akan bayyana nakasun da kuma gazawar gwamnatin jihar mai ci karkashin jagorancin gwamna Nasir El-Rufa'i, da kuma hanyoyin inganta tsaro da ya yi kamari a jihar.

KARANTA KUMA: Obasanjo ne ya kafa tushen mummunan jagoranci a Najeriya - Osogba

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, manema takarar sun hadar da tsohon gwamnan jihar Ramalan Yero, tsohon shugaban hukumar NEMA Sani Sidi da kuma tsohon dan majalisar wakilai, Isah Ashiru da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a kwana-kwanan nan.

Sauran 'yan takarar sun hadar da, Muhammad Kadade, Bello Kagarko, Jonathan Kish, Shu'aibu Mikati, Sani Bello, Ibrahim Dauda, Ja'afaru Sa'ad da kuma Muhammad Sani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel