Yanzu-Yanzu: Osinbajo ya bayyana dalilin da ya sa ya tsige shugaban DSS, Lawal Daura

Yanzu-Yanzu: Osinbajo ya bayyana dalilin da ya sa ya tsige shugaban DSS, Lawal Daura

Labarin da muke samu da dumin sa yanzu daga fadar shugaban kasa ya fayyace mana dalilin da yasa mukaddashin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, watau Farfesa Yemi Osinbajo ya tsige shugaban jami'an tsaron farin kaya na DSS, Lawal Daura.

Bayanan da ke zuwa mana dai sun tabbatar da cewa toshe majalisar tarayyar da jami'an na tsaron farin kaya suka yi shine ya sa mukadasshin shugaban kasar ya harzuka kuma har ma ya tsige shi.

Yanzu-Yanzu: Osinbajo ya bayyana dalilin da ya sa ya tsige shugaban DSS, Lawal Daura
Yanzu-Yanzu: Osinbajo ya bayyana dalilin da ya sa ya tsige shugaban DSS, Lawal Daura

KU KARANTA: Shugaban kungiyar masoya Buhari na kasa yayi murabus

Legit.ng ta samu cewa wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya tafi hutu a kasar Ingila.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tsige shugaban hukumar tsaro ta sirri, wato DSS, Malam Lawal Daura daga mukaminsa biyo bayan farmakin da jami’an hukumar suka kai majalisar dokokin Najeriya da safiyar ranar Talata 7 ga watan Agusta.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Osinbajo, Laolu Akande ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 7 ga watan Agusta.

Haka zalika hadimin shugaban kasa Buhari akan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya tabbatar da fatattakar Lawal Daura daga aiki.

Bugu da kari, Farfesa Osinbajo ya umarci Lawal Daura ya mika ragamar tafiyar da hukumar ga jami’I mafi girma a hukumar, har sai baba ta ji.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel