Najeriya na cikin kasashen da ke asarar jama'arta saboda talauci

Najeriya na cikin kasashen da ke asarar jama'arta saboda talauci

- Asarar da ta kai gurin dala 23,620 na kowane mutum a kasashe 141 ya zamo ta rashin daidaituwar jinsi

A Afirka, asarar an kiyasta zata kai dala tiriliyan 2.5 da kuma sauran kasashen na yankin

Najeriya na cikin kasashen da ke asarar jama'arta saboda talauci
Najeriya na cikin kasashen da ke asarar jama'arta saboda talauci
Asali: Depositphotos

Wani tsohon Chiyaman din United States Federal Reserve kuma masani a fannin tattali, Ben Bernanke ya taba cewa :"Samu mabambamci yana kawo matsala saboda yana nufin mutane sa yawa a al'umma basu da damar samun cigaban kansu,... Babu wata daula da zata cigaba ba tare da ingantatattun ma'aikata ba, ballantana kuma a wannan zamani na canjin fasaha, "

Marigayi Nelson Mandela ya kara da cewa :" Matukar talauci, rashin adalci da bambanci yayi yawa a duniya, babu wani daga cikin mu da zai huta,... "

Wadannan kalubalen ana samun su ne kasashe masu habakowa, Najeriya ma ba a barta a baya ba.

A kowacce shekara, ittifakin rashin daidaituwa yana kara hauhawa.

Wani sabon rahoton bankin duniya yace tsakanin dala tiriliyan 15 da dala tiriliyan 30 ne ake asara kuma dama kadan ake samu gurin ilimantar da yara mata na shekaru 12 na farkon rayuwa.

DUBA WANNAN: Harin Boko Haram a Maiduguri

Kwanan nan ne kungiyar bankin duniya, a rahoton ta mai taken :"Unrealised Potential :The high cost of Gender Inequality in Earnings, " yace kusan kasashe 141 ne suke asarar dala tiriliyan 160 na arzikin su saboda nuna bambanci, wanda yake kawo rashin daidaituwar samu a tsakanin mata da maza.

Asarar da ta kai gurin dala 23,620 na kowane mutum a kasashe 141 ya zamo ta rashin daidaituwar jinsi.

A Afirka, asarar an kiyasta zata kai dala tiriliyan 2.5 da kuma sauran kasashen na yankin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel