Wayyo: Ciwon kafa ya kama matashin nan da ya je Abuja a kasa saboda Buhari

Wayyo: Ciwon kafa ya kama matashin nan da ya je Abuja a kasa saboda Buhari

A shekarar 2015 ne Abubakar Duduwale, masoyin shugaba Buhari, ya taka da kafar sa daga Yolan jihar Adamawa zuwa Abuja domin ya halarci rantsar da Buhari.

Duduwale ya bayyana cewar ya yi tattakin ne domin nuna jin dadinsa da nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben shekarar 2015, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya Walla.

Kafafen yada labarai da suka hada da gidan talabijin na kasa (NTA) sun nuna tattakin na Duduwale a ranar da ya bar Yola.

Wayyo: Ciwon kafa ya kama matashin nan da ya je Abuja a kasa saboda Buhari
Abubakar Duduwale

Wayyo: Ciwon kafa ya kama matashin nan da ya je Abuja a kasa saboda Buhari
Abubakar Duduwale

Duduwale, dan kabilar Chamba daga karamar hukumar Yola ta Arewa, ya fara tattakin na shi ne daga kofar garin Yola dake kan babban titin Yola zuwa Numan da misalin karfe 6:30 na safe.

DUBA WANNAN: Allah Buwayi: Dattijuwa mai shekaru 60 ta haihu bayan shekaru 30 da aure (Hotuna)

Shekaru uku bayan ya yi wannan bajinta, Duduwale ya gamu da lalurar ciwon kafa kamar yadda hotunansa da suka mamaye kafafen sada zumunta suka tabbatar.

Wani ma'abocin amfani da shafin sada zumunta na Tuwita @GASSA01 ya saka hoton Duduwale tare da bayyana cewar yanzu haka ya nakasa kuma yana matukar neman taimako.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel