Yanzu Yanzu: Mataimakin gwamnan Akwa Ibom yayi murabus, ya koma APC

Yanzu Yanzu: Mataimakin gwamnan Akwa Ibom yayi murabus, ya koma APC

Pa Moses Ekpo, mataimakin gwamnan jihar Akwa Ibom yayi murabus, kamar yadda shafukan @APCNewspaper da Ibom.com.ng suka wallafa a twitter.

Gwamnatin PDP mai mulki a Akwa Ibom bata tabbatar da hakan ba tukuna, amma APC da Ekpo, mataimakin gwamna mafi dadewa a Najeriya, na kokarin bin sahin Sanata Godswill Akpabio zuwa jam’iyyar All Progressives Congress.

Dukkaninsu makusantan yan siyasa ne. Akipabio tsohon gwamnan jihar da mulki jihar tsawo shekaru takwas (2007-2015) sannan ya daura gwamna mai ci Udom Emmanuel.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Gwamnatin jihar Kano tace Hafiz Abubakar ya ajiye aiki a matsayin mataimakin gwamna a ranar Lahadi domin gujema tsige shi daga kujerarsa.

KU KARANTA KUMA: Mai ba Buhari shawara ya roki ‘Yan Majalisa su hakura da dogon hutu su koma aiki

A wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan bayanai, Muhammad Garba, a yammacin ranar Lahadi, gwamnatin tace Mista Abubakar ya lura da cewa 30 daga cikin 40 na yan majalisar dokokin jihar Kano sun sanya hannu domin fara shirin tsige shi.

Mista Garba yace an so tsige gwamnan saboda zargin karya da zarge-zarge marasa kan gado da ayiwa gwamnatin jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jam'iyyar ADP ta sha alwashin fatattakar APC a zaben Gwamnan wata Jiha a Najeriya

Jam'iyyar ADP ta sha alwashin fatattakar APC a zaben Gwamnan wata Jiha a Najeriya

Jam'iyyar ADP ta sha alwashin fatattakar APC a zaben Gwamnan wata Jiha a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel