Me ya hado Saudiyya da kasar Canada rigima?

Me ya hado Saudiyya da kasar Canada rigima?

- Kasar Saudiyya ta kori Jakadan Kanada daga kasarta

- Kamfanin dillancin labaran kasar ya ce shi ma jakadan Saudiyya a birnin Ottawa na Canada an bukaci ya koma gida

- An yanke huldar kasuwanci tsakanij kasashen biyu

Me ya hado Saudiyya da kasar Canada rigima?
Me ya hado Saudiyya da kasar Canada rigima?

Kasashen Turawa kan yi kokarin gaya wa kasar Saudiyya gaskiya, wadda ke tsarin mmulukiyya ba dimokuradiyya ba.

Ana yawan kame masu fadin albarkacin bakinsu a kasar kuma ana hana su damar kare kansu.

Kasar Saudiyya ta kama wasu masu rajin kare hakkokin mata, duk da kasar Saudiyyar na tauye wa mata hakkoki karkashin tsarin shari'ar Islama.

Kasar Canada mai makwabtaka da AMurka, ta soki kasar Saudiyya wajen kama wasu mata wadanda suka bada gudummawar wayar wa da mata kai har suka sami 'yancin yin tukin mota a kasar a bana.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa Farfesa Hafiz Abubakar ya bar gwamnatin Kano

Saudiyya taji haushin kushen, inda ta kira lammarin da cewa kutse ne cikin lamarin kasar ta, inda ta kori jakadan kasar ta Canada, kuma ta kira nata data jakadan daga kasar da ya dawo gida har warware.

Ta kuma dakatar da harkar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel