Dauki-ba-dadi: Dakarun sojin Najeriya sun yi kicibis da wasu 'yan bindiga a jihar Benue

Dauki-ba-dadi: Dakarun sojin Najeriya sun yi kicibis da wasu 'yan bindiga a jihar Benue

Rundunar dakarun sojin Najeriya dake sintirin tabbatar da tsaro da samar da zaman lafiya a jahohin Arewa ta tsakiya a ranar Asabar din da ta gabata sun sanar da yin kicibis da wasu 'yan bindiga a karamar hukumar Guma ta jihar Benue.

Sanarwar afkuwar hakan dai ta fito ne dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na hedikwatar rundunar dake Abuja, Texas Chuku inda yace kuma dakarun nasu sun yi dauki ba dadi da 'yan bindigar.

Dauki-ba-dadi: Dakarun sojin Najeriya sun yi kicibis da wasu 'yan bindiga a jihar Benue
Dauki-ba-dadi: Dakarun sojin Najeriya sun yi kicibis da wasu 'yan bindiga a jihar Benue

KU KARANTA: Karuwai a Najeriya sun yi barazanar shiga yajin aiki (Dalili)

Legit.ng ta samu cewa haka zalika abubuwan da aka kwace daga hannun 'yan bindigar sun hada da bindigar AK 47 da alburusai da ma mashina guda biyar da sauran su.

A wani labarin kuma, Mummunan hatsarin mota ya rutsa da tsohon mataimakin kakakin majalisar jihar Filato dake a yankin Arewa ta tsakiya mai suna Yusuf Gagdi a ranar Asabar din da ta gabata.

Kamar dai yadda muka samu, hatsarin ya auku ne lokacin da motar da ke dauke da dan majalisar tayi taho-mu-gaba da wata motar dauke da wabi babban jami'in rundunar sojin saman Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel