Mahaifiyar Osama Bin Laden ta yi sharhi bayan shekaru da Mutuwar 'Dan ta

Mahaifiyar Osama Bin Laden ta yi sharhi bayan shekaru da Mutuwar 'Dan ta

Alia Ghanem, Mahaifiyar Osama Bin Laden ta bayyana takaicin ta dangane da yadda Marigayin 'Dan ta ya tafiyar da al'amurran sa na rayuwa kafin ajali ya katse ma sa hanzari a ranar 2 ga watan Mayun shekarar 2011 da ta gabata.

Mahaifiyar ta marigayi shugaban kungiyar Al-Qaeda, ta yi ganawar ta ta farko da wata jaridar Guardian inda ta bayyana cewa babban ɗan ta ya ɗauki wannan salo ne sakamakon wankin kwakwala mai sauyin tunani da ya ara kuma ya yafa.

A yayin ganawar ta da jaridar ta Guardian, Ghanem ta bayyana cewa ta sha fama a rayuwar ta kasancewar ɗan na ta na nesa da ita a ko da yaushe, sai ko shakka babu yaron kirki ne da yake matuƙar ƙaunar ta.

Mahaifiyar Osama Bin Laden ta yi sharhi bayan shekaru da Mutuwar 'Dan ta
Mahaifiyar Osama Bin Laden ta yi sharhi bayan shekaru da Mutuwar 'Dan ta

Ghanem ta bayyana cewa, ɗan na ta na fari ya sauya ne baki ɗaya a yayin da yake karatun sa a jami'ar King Abdulaziz dake Birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya inda ya kammala a fanin nazarin tattalin arziki.

Take cewa, mutanen wannan jami'a ne suka sauya masa tunani da ya zamto tamkar ɗan da ba ita ta haifa ba, sakamakon rashin zayyana ma ta ababen dake gudana a rayuwar sa wanda hankali ko tunanin ta bai kai ga ya zamto abinda ya zama a rayuwa.

KARANTA KUMA: Fashewar Bam ta salwantar da rayukan Mutane 15, fiye da 50 sun jikkata a wani Masallacin 'Kasar Afghanistan

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, Mahaifiyar ta bayyana takaicin ta kwarai da aniyya dangane da yadda rayuwar ɗan ta ta kasance tare da bayyana kaicon ta akan wannan hanya da ya zaba a rayuwar sa.

Legit.ng ta fahimci cewa, Ghanem ta koma kasar Saudiyya da rayuwa a shekarar 1950, inda ta haifi Osama cikin Birnin Riyadh a shekarar 1957, inda bayan shekaru uku da haihuwar sa ta rabu da Mahaifin sa kuma ta auri wani Al-Attas da shima ta haifa ma sa 'ya'ya biyu maza.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel