Ina nan daram a jam'iyyar APC - Gwamna Al-Makura

Ina nan daram a jam'iyyar APC - Gwamna Al-Makura

Gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Umaru Tanko Al-Makura, ya bayyana cewa yana nan daram a jam'iyyar APC kuma ba zai taba bibiyar sahun sauran shugabannin yankin Arewa ta Tsakiya wajen yin hannun riga da jam'iyyar ba.

Ya bukaci mambobin jam'iyyar da dukkanin masu ruwa da tsaki akan kada su sanya damuwa ko tasar hankullan su sakamakon ficewar shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki da sauran wadanda suka raba gari da jam'iyyar.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne ya yanke wannan shawara yayin taron ganawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC reshen jihar da ya gudana a fadar gwamnatin sa dake birnin Lafia.

Al-Makura wanda ya jagoranci taron ya mika godiyar sa ga wadanda suka samu damar halarta tare da bayyana goyon baya da karbuwa gami da sadaukarwar su ta ci gaba da kasancewa cikin jam'iyyar duk da guguwar sauyin sheka dake ci gaba da kadawa.

Ina nan daram a jam'iyyar APC - Gwamna Al-Makura
Ina nan daram a jam'iyyar APC - Gwamna Al-Makura

Gwamnan ya ci gaba da cewa, jam'iyyar APC za ta karbi wannan sauyin sheka a matsayin kaddara mai kyawun gaske tamkar wata hanya ta tankade da rairayen baragurbin dake cikin ta.

KARANTA KUMA: 2019: Kwankwaso, Saraki, Tambuwal za su yi takatar Tikitin jam'iyyar PDP

Ya kuma bayyana goyon bayan jihar sa dari bisa dari da tsayuwar daka dangane da goyon bayan shugaba Buhari da jam'iyyar APC a zaben 2019.

A yayin haka kuma Sanata Abdullahi Adamu ya yabawa gwamnan dangane da wannan taro da ya dauki nauyin gudanarwa tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da goyon baya ga shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel