Kwankwaso ko a mazabar sa ba zai iya lashe zabe ba — Gwamna Ganduje

Kwankwaso ko a mazabar sa ba zai iya lashe zabe ba — Gwamna Ganduje

Yayin da lamurran siyasa ke cigaba da daukar sabon salo a jihar Kano da ke a arewa maso yammacin Najeriya, Gwamnan jihar mai ci yanzu, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce tsohon gwamnan kuma Sanata a yanzu Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ko a mazabar sa ma ba zai iya lashe zabe ba.

A don haka ne ma gwamnan yace ya kamata ma ya dena mafarkin zama shugaban kasa, lamarin da ya bayyana a matsayin marar yiwuwa ko kadan.

Kwankwaso ko a mazabar sa ba zai iya lashe zabe ba — Gwamna Ganduje

Kwankwaso ko a mazabar sa ba zai iya lashe zabe ba — Gwamna Ganduje

KU KARANTA: Saraki ya zayyana dalilai 7 da suka sa ya bar APC

NAIJ.com dai ta samu cewa tsohon gwamnan jihar ya fice daga jam'iyyar ta PDP ne tare da wasu sauran Sanatoci a kwanan baya a zauren majalisar ta dattijai.

A wani labarin kuma, Kotun kasa-da-kasa ta International Criminal Court (ICC) a takaice ta fito ta karyata batun da fadar shugaban kasar Najeriya tayi na cewa ta gayyace shugaban kasar ne ya gabatar da makalar sa a kotun saboda tsabar gaskiyar sa.

A baya dai in mai karatu zai iya tunawa, dan majalisar wakilan nan kuma na hannun damar shugaban kasa, Abdulmumini Jibrin da kuma hadiman shugaban kasar suka ce a lokacin cewa wai tsabar gaskiyar shugaban kasar ne ta sa kotun ta gayyace shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Karancin albashi: Kungiyar kwadago ta shirya yi ma gwamnati bore

Karancin albashi: Kungiyar kwadago ta shirya yi ma gwamnati bore

Karancin albashi: Kungiyar kwadago ta shirya yi ma gwamnati bore
NAIJ.com
Mailfire view pixel