Labarin dakarun matan Afirka da suka yaki Turawan mulkin mallaka

Labarin dakarun matan Afirka da suka yaki Turawan mulkin mallaka

Wadannan mata sun taka gagarumar rawa a Masarautar Dahomey wacce take da karfin tsiya a lokacin, wadda a yanzu ita ce Jamhuriyar Benin

Labarin dakarun matan Afirka da suka yaki Turawan mulkin mallaka
Labarin dakarun matan Afirka da suka yaki Turawan mulkin mallaka

Wadannan mata sun taka gagarumar rawa a Masarautar Dahomey wacce take da karfin tsiya a lokacin, wadda a yanzu ita ce Jamhuriyar Benin. A wancan lokacin sune masu kula da Sarki, kuma jarumai ne da basu da tsoro ko kadan, domin kuwa sun samu horon yaki na musamman.

Wadannan mata sun sanya tsoro da yawa a zukatan Turawan mulkin mallaka. Ana fara koya musu dabarun yaki tun suna yara, sai a mai dasu dakaru idan suka zama 'yan mata, inda Sarki da kanshi zai zabe su saboda karfinsu da kuma kyansu.

DUBA WANNAN: Kotu ta sanya ranar da zata sako Zakzaky

Duk lokacin da zasu fita filin daga wani Bawa ke rakasu da kararrawa a hannu yana kadawa, domin sanar da mutane cewa su basu hanya.

A wuraren shekarun 1800, kusan sama da mata 4,000 sukan shiga yaki don fadada masarautar ta Dahomey. A duk lokacin da suka fita filin daga sukan rera wakoki, a cikin wakokin nasu sukan sanya wani buri na son yiwa maza zarra ta kowanne bangare.

Sunyi yaki sosai a lokacin zuwan Turawan mulkin mallaka, Faransawa sunyi ta kara karfinsu a Dahomey.

A shekarar 1890, Sarkin Behazin ya bada umarnin a kai wa dakarun Dahomey mata hari. Bayan an shafe sa'o'i ana gwabza kazamin yaki a tsakanin su, a karshe an tursasawa matan janyewa daga filin daga.

Kasar Faransa ta samu nasara a yakokin da suka biyo bayan wannan a shekarar 1892 a Dahomey. Hakan ne ya kawo karshen Masarautar Dahomey da dakarun mata, amma har yanzu ana tunawa dasu ta hanyar raye - rayen al'ada da ake yi a Jamhuriyar Benin a yau.

Akwai wani sabon Fim da a yanzu ake shiryawa wanda shahararrun 'yan fim dinnan Vioka Davis da Lupita Nyong'o za su fito a ciki, wanda za a shirya shi akan tarihin gwarazan matan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel