Zafafan tambayoyin EFCC sun sanya Mataimakin Saraki fara rashin lafiya

Zafafan tambayoyin EFCC sun sanya Mataimakin Saraki fara rashin lafiya

- An dage tuhumar mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu ta zama kwantai

- Ba jimawa bayan fara masa tambayoyi ne aka ga yana rawar dari

- Don haka ne EFCC suka amince masa tafiya asibiti a duba lafiyarsa

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu ya kamu da rashin lafiya a lokacin da hukumar EFCC ke tsaka da tuhumarsa.

Tambayar kaka uwarka ta haifeka: Mataimakin Saraki ya fara rashin lafiya a hannun EFCC
Tambayar kaka uwarka ta haifeka: Mataimakin Saraki ya fara rashin lafiya a hannun EFCC

Tun da farko dai ana zargin Ike Ekweremadu ne bisa mallakar wasu kadarori a cikin kasar nan da kasar Birtaniya da kuma hadaddiyar daular larabawa wato Dubai. Hukumar ta bukaci ya yi mata karin haske akan yadda akai ya mallaki wadannan kadarori a ciki da wajen kasar nan, wadanda adadin su ya zarta 60.

KU KARANTA: Iyalan Dasuki sun kai ministan shari'a AGF Malami kara

Bayan fara tuhumarsa a ofishin hukumar a jiya, sai suka ga alamun rashin lafiya sun bayyana a tattare da Ekwemeradu, hakan ya sanya aka sallame shi domin tafiya asibiti don a duba lafiyarsa.

Wata majiya daga hukumar ta EFCC ta bayyana cewa sun kara gano adadin wasu kadarorin mallakin mataimakin shugaban majalisar dattawan.

"Muna da adadin kadarori guda 38 wanda za su bamu damar bincike, sai kuma ga shi mun sake gano adadin wasu kadarorin guda 22, suka zama 60 cif".

"Lokacin da mu ka fara sauraron bayanin amsoshin tambayoyin binciken da mu ke masa, sai muka lura ba shi da koshin lafiyar da zai iya cigaba. Dole ya sa muka sallame shi domin neman lafiyarsa". Majiyar ta shaida.

Idan za'a iya tunawa dai gwamnatin tarayyar kasar nan ce ta kafa wani kwamiti na musamman domin bincikar yadda akai tasarrafi da dukiyar kasar nan, inda kwamitin ya binciko wadannan kadarori mallakin shugaban majalisar dattawa, wadanda ake ganin ya mallake su ne ta haramtacciyar hanyar.

Kawo yanzu hukumar ta bayyana cewa cigaba da sauraron mataimakin shugaban majalisar dattawan na da alaka da samun cikakkiyar lafiyarsa.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel