Wadanda su ka sauya-sheka sun cin amanar al’ummar Najeriya kuma sai sun ciza yatsa – Gudaji Kazaure

Wadanda su ka sauya-sheka sun cin amanar al’ummar Najeriya kuma sai sun ciza yatsa – Gudaji Kazaure

Labari ya same mu cewa ‘Da Majalisar da ke wakiltar Yankin Kazaure da kewaye watau Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure yayi Allah-wadaran ‘Yan siyasan da su ka fice daga Jam'iyyar APC.

Wadanda su ka sauya-sheka sun cin amanar al’ummar Najeriya kuma sai sun ciza yatsa – Gudaji Kazaure
Gudaji Kazaure ya soki wadanda su ka koma PDP

Hon. Gudaji Kazaure wanda yake ikirarin yana tare da Shugaba Buhari ya bayyana cewa son rai ne ya sa wasu manyan ‘Yan siyasar kasar nan su ka fice daga Jam’iyyar APC mai mulkin kasar su ka koma Jam’iyyar adawa ta PDP.

‘Dan Majalisar na Kazaure/Roni/Gwiwa/M-kwashi yayi wata hira da ‘Yan jarida inda yayi magana game sauya-shekar da wasu su kayi. Kazaure yace duk wadanda su ka bar APC sun yaudari Talakawan da su ka zabe su a 2015.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta rasa manyan 'Ya 'yan ta a Jihar Sokoto

Muhammad Gudaji Kazaure ya nemi al’umma su guji wadanda su ka fice daga APC idan zaben 2019 ya karaso. Kazaure ya bayyana cewa wadanda su ka koma PDP a yanzu bayan sun soki Jam’iyyar a baya sun yi baki biyu.

‘Dan Majalisar na Jihar Jigawa ya nuna bacin ran sa game da yadda wasu su ka bar Jam’iyyar APC. Kazaure ya tabbatar da cewa duk wadanda su ka bar APC za su yi da-na-sanin abin da su kayi inda yace su su na bayan Buhari.

Dama kun san cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Magoya bayan sa sun sauya-sheka daga APC a jiya da yamma. Dazu ma kuma Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu sun koma Jam’iyyar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel