Sauya sheka: PDP ta yiwa Tambuwal barka da dawowa gida

Sauya sheka: PDP ta yiwa Tambuwal barka da dawowa gida

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yiwa gwamnan jihar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal barka da zuwa jam’iyyar.

A ranar Laraba, 1 ga watan Agusta gwamnan ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP.

Jam’iyyar ta wallafa sakon a shafinta na twitter jim kadan bayan gwamnan ya sanar da sauya shekar tasa.

Sauya sheka: PDP ta yiwa Tambuwal barka da dawowa gida

Sauya sheka: PDP ta yiwa Tambuwal barka da dawowa gida

Ta ce: “Labari da dumi-dumi! Gwamnan jihar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal @AWTambuwal ya sauya sheka daga gajiyayar jam’iyyar @APCNigeria zuwa @OfficialPDPNig. Muna masa barka da dawowa gida."

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a ranar Talata ya hadu da magoya bayansa a Ilorin, inda anan ya fada masu cewa ya bar jam’iyyar All Progressives Congress saboda jajircewarsu akan ya aikata hakan da kuma shige masa gaba da Allah yayi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kama shugaban INEC, Mahmoud

Ya ci gaba da zargin cewa an nuna wariya ga jihar Kwara wajen nade-naden da gwamnatin APC ke yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa
NAIJ.com
Mailfire view pixel