Kashe-kashen Zamfara: Sojin saman Najeriya sun kaddamar da rundunar 'Dirar mikiya'

Kashe-kashen Zamfara: Sojin saman Najeriya sun kaddamar da rundunar 'Dirar mikiya'

Rundunar sojojin saman Najeriya watau Nigerian Air Force, NAF sun sanar da cewa yanzu haka jami'an ta da kuma jiragen yaki da dama sun fara sauka a dazukan jihar Zamfara a karkashin wata runduna da suka dabbaka mai suna 'Dirar mikiya'.

Mista Olatokunbo Adesanya dake zaman jami'an hulda da jama'a na rundunar shine ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Abuja.

NAIJ.com ta samu dai cewa rahotanni daga jihar Katsina na nuni ne da cewa tuni jiragen yaki suke ta shawagi a saman inda suke ta kawo jami'an soji da kuma kayayyakin yaki a mani mataki na cika umurnin shugaban kasa.

A wani labarin kuma, Wani rahoto da muke samu daga kafofin sadarwar zamani sun tabbatar mana da cewa jami'an 'yan sandan Najeriya a jihar Kano sun cika hannuwan su da wasu mabiya darikar kwankwasiyya a jihar.

Kamar dai yadda muka samu, yan sandan sun ce laifin da wadanda suka kama din da galibin su matasa ne shine na kona tsintsiya a bainar jama'a.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jam'iyyar PDP ne neman a tsige Sanatanta da ya sauya sheka zuwa APC

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Sanata Akpabio

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Sanata Akpabio
NAIJ.com
Mailfire view pixel