Da na koma PDP gara na bar siyasa - Tsohon gwamnan jam'iyyar

Da na koma PDP gara na bar siyasa - Tsohon gwamnan jam'iyyar

- Tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Kalu, ya bayyana cewar ba zai taba komawa jam'iyyar PDP ba

- Ya bayyana cewar ba ya shirin fita daga APC komawa PDP

- Kalu ya kara da cewa APC ce kadai jam'iyyar da zata iya tsamo Najeriya daga halin da gwamnatin baya ta jefa ta

Tsohon gwamnan jihar Abiya a karkashin jam'iyyar PDP, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewar bashi da niyyar fita daga jam'iyyar APC mai mulki.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar gwamnan, ta bakin Kunle Oyewumi, mai taimaka masa a bangaren yada labarai, ya yi watsi da jita-jita dake yawo a gari kan cewar ya gama shirin komawa PDP.

Kalu ya bayyana rahoton, da wasu kafafen yada labarai na yanar gizo suka yada, da cewar zuki tamallle ce kawai.

Da na koma PDP gara na bar siyasa - Tsohon gwamnan jam'iyyar
Orji Kalu

Tsohon gwamnan ya kara da cewar babu abinda zai mayar da shi PDP tare da bayyana cewar gara ma ya hakura da siyasa bakidaya a kan ya koma jam'iyyar ta PDP. Kazalika ya shawarci masu kirkirar labarai na karya da su nemi sana'ar kirki.

A jiya, Talata, Legit.ng ta kawo maku labarin cewar wata babbar kotu dake Legas tayi watsi da matakin da tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, ya dauka na shaida mata cewar ba bu tuhumar da zai amsa daga zargin almundahanar da ake yi masa.

DUBA WANNAN: Almundahana: Sai fa ka amsa tuhumar EFCC - Kotu ta sanar da tsohon gwamnan PDP

Hukumar yaki da yiwa tattalin arziki ta’annati (EFCC) ce ta gurfanar da Kalu tare da wani kamfaninsa bisa zargin karkatar da kudin jihar Abiya, biliyan N2.9bn, lokacin da yake gwamna daga 1999 zuwa 2007.

Kalu ya kafe kan cewar bai aikata ko daya daga cikin laifukan da ake tuhumarsa da su ba, a saboda haka babu wata tuhuma da zai amsa dangane da batun zargin shi da almundahana, Lamarin ya jawo tsaiko a shari’ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel