Bamu da niyan barin jam’iyyar APC – Gwamnonin Adamawa da Niger

Bamu da niyan barin jam’iyyar APC – Gwamnonin Adamawa da Niger

Gwamnan jihar Adamawa, Mohammed Bindow, da takwaransa na jihar Niger, Abubakar Bello, sun yi watsi da rade-radin dake yawo cewa suna kokarin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Gwamnonin sun bayyana matsayarsu a wani zantawa da suka yi da manema labarai a lokuta daban-daban a jihohinsu.

Bindow yayi Magana a yayinda yake amsa wata tambaya akan lamarin a lokacin day a dawo Yola, babban birnin jihar bayan wani ziyara da ya kai Abuja a ranar Litinin.

Bamu da niyan barin jam’iyyar APC – Gwamnonin Adamawa da Niger
Bamu da niyan barin jam’iyyar APC – Gwamnonin Adamawa da Niger

Gwamnan yayi bayanin cewa duk da tarin sauya sheka da ya tunkari APC a matakin tarayya, jam’iyyar na da karfi a jihar Adamawa.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje yayi magana akan tsige kakakin Kano

Da yake jawabi a nasa bangaren, takwaransa na jihar Niger, Abubakar Bello ya fadawa majiyarmu cewa babu dalilin da zai sa shi barin jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel