Ka shirya tattara kayanka, zamu tashi kiyamar siyasarka a 2019 – APC ga wani Sanatan Arewa

Ka shirya tattara kayanka, zamu tashi kiyamar siyasarka a 2019 – APC ga wani Sanatan Arewa

- Sauya sheka yana kara dugunzuma siyasar kasar nan gabannin zaben 2019

- A jihar Kaduna jam'iyyar APC ce ta lashi takobin yiwa wani Sanata ritaya daga siyasa baki daya

- Wannan na zuwa bayan ya sauya sheka zuwa PDP

Da alama jam’iyyar APC bata ji dadin kalaman da Sanata Suleiman Hakunyi yayi ga gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasiru El-rufa'I ba, na cewa zai fitar da shi daga fadar gwamnatin jihar Kaduna a zaben Shekarar 2019.

Ka shirya tattara kayanka, zamu tashi kiyamar siyasarka a 2019 – APC ga wani Sanatan Arewa
Ka shirya tattara kayanka, zamu tashi kiyamar siyasarka a 2019 – APC ga wani Sanatan Arewa

Wannan ne karon farko da jamiyyar ta mayar da martani a karon farko akan ficewar da Sanata Suleiman Hunkuyi yayi daga Jamiyyar, cikin wata sanarwa da mataimakin yada labaran jamiyyar Salisu Wusono ya rattabawa hannu.

Sanarwar ta kara da cewa wannan ba sabon abu bane a tarihin siyasar sa, domin tun a shekarar 2003 ya gaza kai bantensa a lokacin da ya bar jamiyyar PDP zuwa APP, inda ya yi takarar gwamna amma bai kai ga nasara ba.

"Bai taba cin zabe ba a tarihin siyasarsa, sau nawa yana faduwa? Ya kamata Sanata Hunkuyi ya godewa jamiyyar APC domin da farin jininta ya yi amfani wajen nasarar lashe zaben da ya kai shi ga majalisar dattawa" In Ji Wusono.

KU KARANTA: Ni da Kwankwaso ne jagororin PDP a Kano - Shekarau

Ya kara da cewa al'ummar jihar Kaduna shaida ne, domin tun a Shekarar 2017 Sanata Hunkuyi ya ke ikirarin shi ne jagoran jamiyyar APC a jihar kuma babu wani dalilin da zai sa ya fice daga Jamiyyar.

Ka shirya tattara kayanka, zamu tashi kiyamar siyasarka a 2019 – APC ga wani Sanatan Arewa
Ka shirya tattara kayanka, zamu tashi kiyamar siyasarka a 2019 – APC ga wani Sanatan Arewa

"Akwai bukatar Sanata Hunkuyi ya fahimci cewa nasarar da gwamna El-rufa'i da kuma shugaban kasa Muhammad Buhari suka samu daga Allah take, tare kuma da goyon bayan al'umma wanda hakan ya sa Sanata Hunkuyi ya shiga Alfarmarsu har ya kai ga nasara".

"Ya kamata Sanata Hunkuyi ya yiwa al'ummar jihar Kaduna bayanin me ya raba shi da tsohon gwamnan jihar Ahmed Makarfi, da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo da sauran manyan ‘yan siyasa".

"Al'ummar jihar Kaduna sun ajiye dukkanin wani cin amanar siyasa da Sanata Hunkuyi ya yi, kuma sai sun yi masa ritiyar gaba daya a fagen siyasar jihar da ma kasa baki daya". APC ta bayyana.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel