'Yan kabilar Ibo suna so addinin musulunci ya mamaye yankin su a Najeriya

'Yan kabilar Ibo suna so addinin musulunci ya mamaye yankin su a Najeriya

Shugaban hukumar jin dadin alhazai a jihar Ebonyi dake a shiyyar kudu maso gabshin Najeriya, Alhaji Abas Egwu ya nuna sha'awar sa game da yadda yace suna bukatar addinin musulunci ya yadu sosai a kudancin kasar.

Kamar yadda muka samu, Alhaji Egwu ya bayyana hakan ne lokacin da yake fira da manema labarai jim kadan tattaunawar sa da babban sakataren kungiyar the Ansar-Ud-Deen, Alhaji Ibrahim Kilani a garin Abakalki.

'Yan kabilar Ibo suna so addinin musulunci ya mamaye yankin su a Najeriya
'Yan kabilar Ibo suna so addinin musulunci ya mamaye yankin su a Najeriya

KU KARANTA: An kama babbar mota makare da muggan makamai a Arewa

Legit.ng ta samu cewa a don haka ne ma ya ke rokon dukkan musulmai a ko ina suke da su taimaka masu wajen yada musuluncin musamman ma wajen gina makarantun islamiyoyi.

A wani labarin kuma, a wani mataki na samar da dawwamammen zaman lafiya a kasar sa, shugaba Rodrigo Duterte na kasar Filifins ya sanar da baiwa yankin kudancin kasar da ke da mafi rinjayen mabiya addinin musulunci karin ikon cin gashin kai.

Wannan mataki dai kamar yadda muka samu, ana sa ran zai kawo karshen takun sakar dake wanzuwa tsakanin yankin da gwamnatin kasar tare da tabbatar da dawwamammen zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel