Abin da sauyin shekar Kwankwaso ke nufi ga jam'iyyar APC a jihar Kano - Ganduje

Abin da sauyin shekar Kwankwaso ke nufi ga jam'iyyar APC a jihar Kano - Ganduje

Ficewar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso da wasu 'yan majalisa daga jam'iyyar APC, ba zai kawo wata tangarda a gare ta ba ta fuskar siyasa kamar yadda gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne gwamna Ganduje ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a fadar gwamnatin sa, inda ya ce ba ya da wani haufi dangane da ficewar abokin adawar sa ta siyasa daga jam'iyyar.

Yake cewa, ko kadan ba su da wata fargaba dangane da ficewar 'yan majalisar daga jam'iyyar, bugu da kari ma kuma jama'a su bude idanu tare da sauraron abin da zai faru a babban zabe na 2019.

Ganduje ya kuma ce, ba bu wanda ficewar Kwankwaso za ta shafa cikin jihar Kano sakamakon yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke ci gaba da sauke nauyin sa wajen ciyar da kasar nan gaba.

Abin da sauyin shekar Kwankwaso ke nufi ga jam'iyyar APC a jihar Kano - Ganduje
Abin da sauyin shekar Kwankwaso ke nufi ga jam'iyyar APC a jihar Kano - Ganduje

Gwamnan na Kanon Dabo ya kuma bayyana cewa, a yayin da Sanata Kwankwaso ke sanye da riga ta jam'iyyar APC domin neman takarar kujerar shugaban kasa, daga bisani ya fahimci cewa ba ya da wurin zama a fadar shugaban kasa da ta sanya ya yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar.

KARANTA KUMA: Wasu 'Yan sanda sun yi kuskuren harbe wani jami'in SARS har Lahira a jihar Anamba

Ya ci gaba da cewa, Kwankwaso zai fahimci irin mashahuranci da kuma soyayyar da al'ummar jihar Kano ke yiwa shugaba Buhari yayin fafatawa a zaben 2019 muddin ya samu tikitin takara na sabuwar jam'iyyar sa ta PDP.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tsohon gwamnan na jihar Kano na daya daga cikin sanatoci 14 da suka fice daga jam'iyyar APC a ranar Talatar da ta gabata. Ana sa ran zai nemi tikitin takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyar PDP dangane da zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel