Kada ku zargi Shugabanni kadai da laifin yanayin da Najeriya take ciki a halin yanzu - Buhari

Kada ku zargi Shugabanni kadai da laifin yanayin da Najeriya take ciki a halin yanzu - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis din da ta gabata ya nemi 'yan Najeriya akan su daina zargin shugabanni da laifin yanayi da halin da kasar nan take ciki a yanzu.

Shugaban kasar wanda a cikin kwanakin nan ake fama suka tare da caccakar yadda yake gudanar da al'amurran kasar ya bayyana cewa, canjin da kasar nan ta kudirta cimma ba zai tabbatu face kowane mutum guda ya fara assasa sauyi a karan kansa.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabwan sa a taron bikin yaye manyan dakarun soji a cibiyar su ta Forces Command and Staff College dake garin Jaji a jihar Kaduna.

A yayin da fadar ta shugaban kasa ta gabatar da jawabai ga manema labarai a babban birnin kasar nan, shugaba Buhari ya bayyana cewa canji da kowa ke hankoro sai ya fara tabbatuwa kan kowane mutum.

Kada ku zargi Shugabanni kadai da laifin yanayin da Najeriya take ciki a halin yanzu - Buhari
Kada ku zargi Shugabanni kadai da laifin yanayin da Najeriya take ciki a halin yanzu - Buhari

Duk da kasancewar shugaba Buhari ya aminta da sanya babban kaso na laifin yanayin da kasar nan ke ciki a halin yanzu, ya kuma ce dole ne sai al'umma ta takar muhimmiyar rawar gani domin tabbatar da cimma manufar kawo sauyi na ci gaba.

KARANTA KUMA: Almundahana: Shugabannin tsaro da Gwamnoni na yashe N241bn cikin asusun Gwamnati a duk shekara

Shugaban kasar ya sake tabbatar wa da 'yan Najeriya kokari da fafutikar gwamnatin sa wajen dawo da kasar nan cikin yanayi da hali na zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A yayin haka shugaba Buhari ya nemi dakarun sojin akan su mike tsaye tare da jajircewa wajen sauke nauye-nauyen da rataya a wuyan su tare da kare martabar da kasar nan a kowane hali da suka tsinci kansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel