Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari kauyen Jakana, jihar Borno

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari kauyen Jakana, jihar Borno

Wasu yan bindiga da ake kayutata zaton yan Boko Haram ne sun kai mumunan hari Jakana kusa da garin Maiduguri da daren yau Alhamis misalin karfe 9:20.

Jakana wani gari ne da ke hanyar Kano zuwa Maiduguri. Yan Boko Haram basu taba samun nasaran kwace garin duk da hare-haren da yan ta'addan ke kaiwa.

Wata majiya ta bayyanawa jaridar Premium Times cewa maharan sun zo ne da manyan makamai sun kwashe awa daya suna ruwan wuta.

Yace: "A yanzu da nike magana da ku, sai da muka gudu kauyen Kolori saboda yan bindigan sun shigo ta Benishek"

Ya kara da cewa yan Boko Haram sun fara kai hari barikin sojoji ne kafin suka karaso cikin garin Jakana.

Yace: " Ba za mu iya cewa ga iyakan mutanen da suka hallaka ba yanzu saboda har yanzu suna harbe-harbe."

Zamu kawo muku cikakken rahoton...

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jam'iyyar PDP ne neman a tsige Sanatanta da ya sauya sheka zuwa APC

Jam'iyyar PDP ne neman a tsige Sanatanta da ya sauya sheka zuwa APC

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Sanata Akpabio
NAIJ.com
Mailfire view pixel