Wasu Gwamnonin da ke shirin canza shekar siyasa a Najeriya

Wasu Gwamnonin da ke shirin canza shekar siyasa a Najeriya

Yanzu haka dai an soma jan dagan zaben da za ayi a 2019 inda wasu Gwamnoni da ‘Yan Majalisu su ka fara ficewa daga Jam’iyyun da su ke. Yanzu haka ana kishin-kishin din cewa akwai wasu Gwamnonin da za su kuma sauya-sheka.

Wasu Gwamnonin da ke shirin canza shekar siyasa a Najeriya
Akwai Gwamnonin da za su bi sahun Ortom su tsere daga APC

Bayan ficewar Gwamnan Jihar Benuwai Samuel Ortom daga APC, wasu Gwamnonin da ka iya tserewa daga Jam’iyyun sun hada da:

1. Aminu Tambuwal

Kamar dai yadda Gwamnan Benuwai ya samu matsala da Sanatan sa George Akume, ana tunanin rikicin Gwamna Aminu Tambuwal da Sanata Ibrahim Wammako ta kai dole Gwamnan ya tsere ya ba shi wuri. Da alamu Tambuwal ya shirya barin APC zuwa PDP.

KU KARANTA: 2019: An shirya yakar Ganduje gadan-gadan a Jihar Kano

2. Abdulfatahi Ahmed

A makon nan ne wasu manyan ‘Yan Majalisu su ka bar APC wanda daga ciki akwai kusan 10 daga Jihar Kwara. Ana tunani kwanan nan Bukola Saraki shi ma zai fice daga PDP. Idan ta tabbata, zai yi wahala Gwamnan Kwara Ahmed ya cigaba da zama a Jam’iyyar APC.

3. Ben Ayade

Yayin da wasu Gwamnonin ke neman barin APC zuwa PDP, ana zargin cewa shi kuma Gwamnan Jihar Kuros-Ribas ya na neman sauya shekar sa ne daga PDP ya dawo APC mai mulki. Ben Ayade yana da alaka mai kyau da Shugaba Buhari kuma ya dan samu matsaloli da PDP.

Kun san cewa Sanatoci fiye da 10 ne su ka bar APC kwanan nan, daga ciki akwai Sanatocin Bauchi, Jigawa, Adamawa da wasu Sanatoci daga Jihar Kwara. Bayan nan kuma akwai ‘Yan Majalisar Wakilan Tarayya da su ka bi sahu su ka arce zuwa Jam’iyyar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel