Kida ya canza, rawa ya canza: Shekewar Kwankwaso zuwa PDP ya sauya lissafin majalisar dattawa

Kida ya canza, rawa ya canza: Shekewar Kwankwaso zuwa PDP ya sauya lissafin majalisar dattawa

Biyo bayan ficewar wasu gagga gaggan yan siyasan Najeriya dake wakiltar al’ummominsu daban daban a majalisar wakilan har su goma sha biyar, shugabancin majalisar za ta canja, kamar yadda ake cewa idan kida ya canza dole rawa ma ya canza.

Sanannen abu ne cewar kafin ficewar yan majalisun, jam’iyyar APC ce take da rinjaye, inda take da Sanatoci sittin da hudu-64 yayin da PDP keda Sanatoci Arbain da biyu-42, amma wannan lamari da ya faru yai sauya lissafin gabaki daya.

KU KARANTA: Zamanin sauyin sheka: Yan majalisar APC guda 37 sun sheke zuwa PDP

A yanzu haka PDP na da yan majalisu Hamsin da shidda-56, bayan ta samu karin Sanatoci goma sha biyar daga APC, duk da cewa ta sallami Sanata Buruji Kashamu, yayin da APC ke da Sanatoci Arba’in da tara-49, sai jam’iyyar APGA mai Sanata guda daya tilo.

Kida ya canza, rawa ya canza: Shekewar Kwankwaso zuwa PDP ya sauya lissafin majalisar dattawa
Majalisar dattawa

Wannan ta sa ba tare da wata wata ba reshe ya juye da mujiya, inda Sanata Godswil Akpabio daga jam’iyyar PDP, wanda shine tsohon shugaban marasa rinjaye ya zama shugaban masu rinjaye, yayin da Ahmad Lawan na APC ya koma mukamin shugaban marasa rinjaye.

Sanatocin da suka fice daga APC zuwa PDP sun hada da Sen. Shaaba, Sen. Melaye, Sen. Shittu , Sen. Rafiu, Sen. Shehu Sani , Sen. Shitu Ubali, Sen. Isa Misau, Sen. Hunkuyi, Sen. Gemade, Sen. Danbaba, Sen. Nafada, Sen. Monsurat, Sen. Tejuoso, Sen. Nazif da Sen. Kwankwaso.

Sai dai dayake shugaban majalisa y adage sauran zama har sai zuwa ranar 25 ga watan Satumba, wannan yasa ba kammala canza sauran mukaman majalisar ba, amma ana sa ran da zarar an dawo za’a sauya su gaba daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel