Likafa ta cigaba: Kungiyar Izala (JIBWIS) zata gina katafariyar jami’a a jihar arewa

Likafa ta cigaba: Kungiyar Izala (JIBWIS) zata gina katafariyar jami’a a jihar arewa

A yau, Litinin, ne kungiyar Izalatul Bid’a waikamatus Sunnah (JIBWIS) ta sanar da cewar gwamnatin jihar Jigawa ta basu kyautar hekta 65 ta fili domin gina jami’ar karatun addinin Musulunci.

Da yake sanar da hakan yau a wurin wani taron bullo da dabarun tara kudi domin sayan dabbar layya ga masu karamin karfi, shugaban kungiyar JIBWIS, Bala Lau, y ace gwamnatin jihar Jigawa ta basu kyautar filin ne a karamar hukumar Hadejia.

A cewar Lau, kungiyar JIBWIS ta samu takardar kyautar filin ne ta hannun sarkin Hadejia, Mai Martaba Abubakar Maje, tare da bayyana cewar zasu kafa wani kwamiti da zai samar da kiyasin adadin kudin da gina jami’ar zai cid a kuma irin kwasa-kwasan da za a ke koyarwa bayan kamala gina ta.

Likafa ta cigaba: Kungiyar Izala (JIBWIS) zata gina katafariyar jami’a a jihar arewa
Shugaban Kungiyar Izala (JIBWIS); Bala Lau

Lau ya bayyana cewar sun zabi gina jami’ar a Jigawa ne saboda akwai zaman lafiya a jihar kuma ga kusanci da take das hi da jihohin arewa maso gabashin Najeriya.

DUBA WANNAN: Hajjin Bana: Jirgin farko na Alhazan Najeriya ya sauka birnin Madina, duba hotuna

Dangane da yadda kungiyar JIBWIS zata gina jami’ar, Lau ya bayyana cewar kungiyar JIBWIS ta samu kimanin N264m daga sadakar fata da jama’a suka bayar a sallar layya ta bara tare da sanar da cewar sun yi amfani da wani bangare na kudin wajen gina gidan Talabijin na Manara da gidan saukar baki na Gumi da gina wani masallaci da asibiti.

Lau ya yabawa gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa bisa basu kyautar filin da kuma yi masu alkawarin bayar da duk wata gudunmawa domin tabbatar da an samu nasarar gina jami’ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel