A 2019, yan Najeriya za su yi jana’izar PDP – Hadimar Buhari

A 2019, yan Najeriya za su yi jana’izar PDP – Hadimar Buhari

Lauretta Onochie, hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta mutu sannan kuma cewa a 2019, yan Najeriya za su binne ta.

Onochie ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter cewa jam’iyyar ba zata iya kafa jam’iyyar hadin gwiwa ba, a yanzu ta dgara ne da masu sauya sheka daga jam’iyyar APC.

Ta kuma bayyana cewa a shekarar 2019, yan Najeriya za su binne PDP wacce ta rigada ta zamo matacciyar jam’iyyar siyasa.

Ga rubutun nata a kasa:

A halin da ake ciki, kungiyar amintattu da na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP za su yi taron gaggawa a ranar Litinin, 23 ga watan Yuli, domin tattauna bukatun wasu mambobin sabuwar jam’iyyar hadin gwiwa wato Coalition of United Political Parties (CUPP).

KU KARANTA KUMA: 2019: PDP ta kira taron masu ruwa da tsaki na gaggawa kan bukatar R-APC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa taron za su tattauna akan zabar dan takarar shugaban kasa mai karfi guda daya domin yiwa jam’iyyar takara a 2019, da kuma bukatar da wasu yan kungiyar sabuwar APC suka gabatar.

Jam’iyyar ta amince da fitar da dantakara guda daya da zai tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Satar inna-naha da ake yi a Gwamnatin Buhari ta sa ake cin bashi – PDP

Satar inna-naha da ake yi a Gwamnatin Buhari ta sa ake cin bashi – PDP

Satar inna-naha da ake yi a Gwamnatin Buhari ta sa ake cin bashi – PDP
NAIJ.com
Mailfire view pixel