Kiran ruwa babu lema: Fusatattun matasa sun halaka dakarun Soji guda 3

Kiran ruwa babu lema: Fusatattun matasa sun halaka dakarun Soji guda 3

Wasu fusatattun matasa sun kashe jami’an Soji guda uku a kasar Uganda sakamakon zarginsu da jama’an gari suka yi da aikata miyagun ayyuka a ranar Lahadi, 22 ga watan Yuli, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wani jami’in gwamnati, Peter Debele ya tabbatar da kisan, inda yace: “An kashe jami’an Sojoji guda uku, kuma mun kaddamar da bincike don tabbatar da dalilin kisan nasu, mun kwato bindigu guda uku a wajen, tare da kama mutane takwas dake da hannu cikin kisan Sojojin.”

KU KARANTA: Mai laya ya kiyayi mai zamani: Jaruman Kannywood 4 da tauraruwarsu ke haskawa

Rahotanni sun bayyana cewa a kwanakin baya ne gwamnatin kasar Uganda ta haramta ma fararen hula sanya kayan Soji kowani iri a sakamakon yawan ayyukan miyagun mutane da suke yi sanye da kayan Soji.

Da wannan ne al’ummar dake yankin Vurra suka tare wadannan Sojoji sakamakon sun gansu sanye da kayan Soji, inda suke nemi su basu bindigunsu, bayan haka ne sai wasu suka fara yadawa cewa yan fashi ne, daga nan ne suka saukar musu, suka kashesu akan wannan zargi.

Daga karshe gwamnatin kasar ta gargadi jama’a daga daukar doka a hannunsu, inda ta bukaci jama’a dasu dinga kai kokensu ga hukuma don share musu hawaye.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa
NAIJ.com
Mailfire view pixel